TARIHIN SARKIN KANO ALU BABBA KASHI NA 1

0 1,677

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

 

Sarki Aliyu shi ne dan Sarki Abdulłahi Maje Karofi dan Sarki Ibrahim Dabo Basullube. Mahaifiyarsa ita ce Saudatu ‘yar Sarkin Musulmi Aliyu Babba

Aliyu dan Abdullahi Maje Karofi wanda aka fi sani da Alu ya shiga gidan Sarautar Kano ranar Lahadi 12 ga watan Satumbar alib 1894 daidai da 12 ga watan Rabi’ul Auwal 1312 Hijiriyya, kuma a ranar ne aka kori Sarki Tukur ya fita daga gidan saurautar Kano.

Domin haka, Aliyu dan Abdullahi Maje Karofi ya zama Sarkin Kano bayan rasuwar wansa Galadima Yusufu, kuma bayan Yusufawa sun kori Sarki Tukur a yakinsu na basasa da Tukurawa, inda ya tafi kasar Katsina.

Wasu manyan gidajen Fulani na Kano suka fara yi masa mubaya’ a ya zama Sarki tare da goyon bayan masu zaben Sarkin Kano. Daga bisani kuma aka aika wa Sarkin Musulmi a Sakkwato ya tabbatar masa da nadin, musamman ma ganin cewa yarsa ce ta haifi Aliyu.

Sarkin Kano Aliyu ya dauki matakai na tsaro da samar da zaman lafiya da kiyaye mutane daga burbushin yakin basasa. Sarkin Kano Aliyu ya nada wasu manyan sarautu wadanda suka taimaka masa tafiyar da mulkinsa cikin sauki da samun hadin kai.

Wadannan sarautu da ya nada sun hada da:

Waziri: Amadu dan Abdullahi Maje Karofi.
Galadima: Shehu dan Abdullahi Maje Karofi.

Madaki: Kwairanga dan Madaki Umaru Nayaya.
Wambai: Isyaku dan Abdullahi Maje Karofi.

Ciroma: Mamuda dan Abdullahi Maje Karofi.
Dan’iya: Malam Gajere dan Abdullahi Maje Karofi.

Ma’aji: Umaru.
Magajin Malam: Musa dan Abdullahi Maje Karofi.

Santuraki: Muhammadu Nakande dan Abdullahi Maje Karofi.
Sarkin Dawakin Tsakar Gida: Abbas dan Abdullahi Maje Karofi.

Bayan haka kuma Sarkin Kano ya yi wasu sarautu na bayin Sarki kamar haKa.

Sarkin Gaya: Jarmai Dila.
Danrimi: Nuhu.

Shamaki: Harisu
Sallama: Barde
Shatima: Shekarau

A lokacin Sarkin Kano Aliyu, masarautar Kano kuma ta sha fama da yake-yake daga waje. Kanawa sun sha fafatawa da mutanen Damagaran ta Kasar Jamhuriyyar Nijar a yau.

Misali, Sarkin Damagaran Amadu ya taba kawo harin yaki a shekarar 1896 inda Sarkin Damagaran Amadu da kansa ya jagoranci dakarun yakinsa.

Kano dai ta yi yaki da Damagaran har sau biyu, amma dai anci nasara akan Damagaran a hannun Sarkin Kano Aliyu.

Haka kuma a lokacin Sarkin Kano Aliyu ne Turawan Mulkin Mallaka suka cinye Kano a 1903. Turawa sun tara zuwa kasar Kano ne a matsayin masu leken asiri. A irin wadannan tafiye-tafiyen da suke yi Sarkin Kano Alu ya fahimci su turawa ne ba Larabawa ba Kamar yadda wasu suke da’awa.

Asanadiyyar haka ne Sarki Aliyu ya tara Jama’a ya fada masu zai tafi Sakkwato ya Kai ziyara wurin Sarkin Musulmi. Amma Madaki Kwairanga ya hana shi, Sarki kuwa ya tsananta sai ya yi wannan tafiya. Daga nan Sarki ya sa aka tara masa dukkan hakimansa da dagatansa da masu unguwanninsa da sauran manyan mutane da samari majiya karfi don tafiya Sakkwato.

Jama’ar da Sarki ya tafi da su Sakkwato na kan dawaki da masu tafiya a kasa, sun fi mutum dubu goma (10,000). Kuma ya sa aka tara manyan malamai suka dinga addu’o’i kofa-kofa, don kada turawa su shiga garin Kano.

Ashe kaddara ta riga fata, Turawa ma suna gab da isowa Kano. Sarkin Kano Aliyu ya isa Sakkwato a wajejen hantsi Inda mutanen Sarki suka dinga shiga birnin sakkwato har zuwa la’asar.

Duk mutanen gari suka tsinke suna mamakin kasaitar wannan Sarki, ga shi Kuma jikan Sarkin Musulmi Alyu ne.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »