TARIHIN SARAUNIYAR ZAZZAU AMINA KASHI NA BIYU

1 256

TARIHIN SARAUNIYAR ZAZZAU AMINA KASHI NA BIYU 

A kashi na daya muntsaya a

Daular Songhai ta kawo mamaya kasar hausa a wannan tsakani, garuruwan kano, katsina da Bornu kuma sun zamo manyan abokan gaba ga zazzau. Don haka akace kasar zazzau ta zamo tana matukar bukatar jarumin shugaba a koda wanne lokaci. Akan haka ne Amina ta gaji sarauta.

Zamu Dora

 Duk da kasancewar ta mace, ta zamo jaruma abar tsoro ga sadaukai. Tun tana karama ake ganin alamomin sadaukantaka a tare da ita har girman ta. Don haka lokacin da ta hau kan mulki tayi gadon Bakwa wanda yayi mulki na shekaru goma, bata samu turjiya daga Sadaukan fadar zazzau ba.

Ance watan Amina ukku akan gadon sarauta ta fara fita yake-yake, inda tarinka cinye garuruwa da yaki tana fadada garin ta.

A wata fadar ma ance kafin tabar mulki, saida ta tursasa sarakunan Kano da katsina su rinqa biyanta Haraji domin su zauna lafiya. Koda yake wani zancen ya ruwaito cewa Amina ta fuskanci matsananciyar turjiyar yaki daga wani Sarki mai suna Kanejeji, sarkin da Littafin Tarihin kano mai taken ‘ wakar Bagauda’ ya ruwaito a matsayin Sarkin Kano na 14 a jerin Sarakunan habe.

Amina batayi sarautar zazzau ba, kurum Shugabar mayakan zazzau ce wadda sunanta ya daukaka. Turawa kuwa sun rubuta tarihinta daruruwan shekaru da suka gabata.

Idan aka koma ga maganar zuriyar sarauniya Amina, a gaskiya abu ne mai wuya ace ga waɗansu da suke zuriyarta ne,.

Kafin rasuwarta babu wani Tarihi daya nuna cewa sarauniya Amina ta tabayin aure, inda tace muddin tayi aure, ta san zata rasa karfin iko irin na mulki,  amma dai Tarihi ya nuna cewa  idan ta ci gari da yaki, sai ta zabo namiji karfaffa ta kwanta da shi, gari na wayewa sai ta kashe shi, saboda kada ya ba kowa labarin ta.

Karanta:

  1. Abusufiyan says

    Your Comment yes

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »