TARIHIN BAYAJIDDA KASHI NA BIYU

0 548

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Kasar Hausa
A KASHI NA DAYA MUNTSAYA A
Bayan yasha ruwan ya isheshi  sai kuma ya dauki kan Macijiyar yasanyashi acikin jakarsa ya koma gidan tsohuwar (Wanda yanzu haka Rijiyar tazama abin kallo). 
ZAMU DORA
Washegari da safe mutane suka taru suna mamakin kashe wannan macijiya, Sarauniyar garin Mai suna Magajiya Daurama tasa akayi sanarwar cewa duk Wanda ya kawo kan wannan macijiya zaayi masa kyauta,  Mutane dayawa sukaita kawo kan maciji Ana gwadawa baiyi daidai ba Ana Cikin wannan yanayi saiga wannan tsohuwa Wanda Bayajidda ya sauka a gidanta t shaidawa Sarauniyar cewa bakonta ne ya kashe wannan macijiya. 
Bayan wannan tsohuwa ta gabatar da bayajidda ga  sarauniyar su Mai sun Magajiya  Daurama sai ta bukaci bayajidda da ya kawo kan macijir ya fito da kan macijiyar ana guwadawa yay daidai wannan dalili yasa tace yan garin suka bukaci ta auri Bayajidda. 
Sarauniya Daurama ta yarda ta auri Bayajidda domin nuna godiyarta, amma da sharadin bazata yi kwanciyar aure dashi ba sai ta hada wasu tanade tanade na al,ada. Saboda haka ta bashi baiwa mai suna Bagwariya kafin lokacinda zata qare tanade tanadenta na al,ada. 
Kwanci tashi bagwariya ta dauki ciki ta haifi da namiji abunka da mata sai ta sawa dan suna Karap da Gari ko kuma Karabagari, wannan abu ya sosawa sarauniya Daurama rai, tana ganin wato tunda ita bata da danamiji To danta zai kar6i sarautar gari kenan, don haka da ta qare tanade tanaden al,ada ta samu ciki ita ma ta haifi da namiji sai ta samashi suna “Bawo” kamar ace kawo kenan a yanzu.
Samuwar Hausa Bakwai:
Don haka Dan gidan Bayyajidda Wanda Sarauniya Magajiya Daurama ta Haifa Mai suna Bawo shine ya haifi yaya shida da Kuma Biram Dan Gimbiya yar Sarkin Barno Da Bayajidda ya aura yatahu da ita zuwa Garin Gabas ( Hadejia a yanzu )  suka mulki wadannan garuruwa kamar Haka:
1. Daura
2. Kano
3. Katsina
4. Zauzzau
5. Gobir
6. Rano
7. Biram ( Hadejia Jihar Jigawa) 
Samuwar Banza Bakwai
Don haka Wannan baiwa da Sarauniya Magajiya Daurama tabawa Bayajidda Mai suna Bagwariya to wannan Bagwariya itace ta haifi da Mai suna Karap Da Gari ko kuma Karabagar shikuma ya haifi yaya Bakwai suka mulki garuruwa kamar haka:
1. Zamfara
2. kebbi
3. Yauri 
4. Gwari ( Jihar Gwarawa)
5. Kwararafa ( Jihar Jikunawa) 
6. Nupe (Jihar Nufawa) 
7. Ilorin (Kasar Yarabawa) 
Karanta:

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »