Bani Da Lafiya Kashi Na Sittin Da Takwas (68)

0 541

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Lokacin muhadarar yayi kuma jama’a sun cika makil a wuirn kuma komai cikin tsari saboda an tanadi wurin zaman maza dabam da kuma wurin zaman mata ma dabam, malamai duk sun halarta da masu gabatar da su.

Bareerah da Labeeba suka zauna a wuri daya tare da iyayensu da kuma sauran jama’ar da suka gayyato, kowa na suararon mai gabatarwa a lokacin da yake gabatar da maluman.

Aka gabatar da Malami na farko bayan ya yi muqaddima sai kai tsaye ya shiga bayani yana cewa:

Kambun-baka ko Kambun-Ido, Nassi ya yi bayaninsa kamar yadda itama Hassada akayi bayaninta, kuma duk an bayyana mana irin illar da Kambun-baka yake yi ga lafiyar mutane domin yana iya hallakar da mutum ( ya kashe mutum) ko kaga mutum yayita fama da rashin lafiya mai tsanani.

Addini ya koyar da mu hanyoyin da za mu nemi ALLAH ya kare mu daga sharrin dukkanninsu da ma masu yin su gaba daya, mu nemarwa kanku, iyalanku, dukiyarku da duk wata ni’imar ku da kukasan kuna da ita kariya da tsarin ALLAH Ubangijin kowa da komai kuma mai iko akan kowa.

Sai Mai gabatarwa yayiwa malamin tambaya yana cewa: Shin Mallam menene Kambun-baka kuma mecece Hassada kuma ya bambancin dake tsakanin su yake ? Saboda mutane suna kishin ruwan sanin wadan nan bayanan cikin ikon ALLAH.

Malamin yace: Ai duk mai Kambun-baka to mai Hassada ne, amma ba ko wanne mai hassada ne yake iya zama mai Kambun-baka ba, saboda kamanceceniyarsu ne ma yasa duk inda kaga an nemi tsari da Hassada ( A nassi ) ba’a ambaci kambun baka ba to ana nufin har da Kambun-Bakan saboda yanayin tasirin su akan al’umma ko a jikin mutane yana zuwa daya ne a lokuta mayawaita.

Kuma shi Kambun-baka ko Kambun-Ido asalinsa yana faruwa ne ta hanyar kallon wani abu wanda zuciyarka ta qullaceshi kuma take nuna masa tsana da kyamar taga wata ni’ima ta same shi.

Amma ita Hassada tana kasancewa ne wajan kaji zuciyarka tana burin afkuwar wani mummunan abu akan wani ko akan wata ni’imarsa.

Kuma tasirin Kambun-baka zai iya faruwa ne akan makusantan mai Kambun-baka ko iyalansa koma dukiyarsa, ko kuma masoyinsa, amma ita Hassada bata afkuwa akan kowa sai wanda zuciyarka take cike da tsanarsa ko kyamar taga wani abu ko wata ni’ima ta same shi.

Mai gabatarwa yakara tambaya yana cewa: Shin Mallam tayaya kuwa mutum zai yiwa kansa ko iyalansa ko dai wani masoyinsa Kambun-baka kuma yayi tasiri akan shi duk da kuwa ya san ba abune na Alkhairi zai sameshi ko zai samesu ba?

(Insha ALLAH a rubutu nagaba za muji ci gaban rubutun.)

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)

Domin karin bayani:

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »