Rayuwar Fateema ( Kashi Na 2 Hausa Novel )

0 130

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

RAYUWAR FATEEMA part 2 (True Life Story)


PART 2

Umma ta gargadi mu akan kada mu sake mu fadawa
yayanmu Mujaheed halin da muke ciki kuma kada mu sanar dashi cewa abba ne ya hanamu
zuwa visiting dinsa Abba ya shigo gida Phateema ta tashi
domin tarar
abbanmu takarasa da sauri ta tsugunna agaban shi tace
abba sannu da zuwa, ya juyo ya daka mata wata harara
ke dalla can munafuka tashi ki bani waje Phateema ta tashi
jikinta a sanyaye,

umma wadda take zaune ranta yai
matukar baci amma abinka da mai hakuri sai dai kawai
tace allah ya kyauta axuciyarta, Phateema ta fada jikin umma
tana kuka tana cewa umma me mukayiwa abba baya son
ganin mu? Umma tace yi shiru kinji “yata ba laifinsa bane
akwai makircin amarya acikin wannan shirin amma Allah
zaiyi mana magani, Phateema taci gaba da rusa kuka ba
kakkautawa umma tana lallashinta,

Na gama shirin
makaranta kaf domin yaune zamu zana english waec
dinmu naxo gurin abba ya tsugunna nace abba aban
kudin makaranta abban namu ya kalleni sannan yasa
hannu a aljihu ya dauko naira ₦50 ya mika mani, Nace
abba ai ₦500 kake bani ₦50 baxata kaini ba, amarya ta
daka mani tsawa kai!! Shashasha mahaifinka ya baka kudi
kace yayi maka kadan? Abba yace kai tashi kaba mutane
waje, Na tashi nayi waje, zuciyata cike da tsanar amarya,
Amarya ta kalli abba tace Honey gobe kannena zasu zo,
abba yace su nawane? Su biyu ne zadai, abba yace to ai
inbanda abinki kamata yayi ace sunfi haka yawa nan
agidansu ne, amarya honey ai akwai wasu xasu xo suma
amma sai nan gaba, abba yace to gskya yakamata suxo da
Hafsat nan da kike ta bani labari, amarya ai ita da Aliyu
xasu xo, abba yace to allah ya kawo su lpy,

ameen amarya tace, Can kuwa bangaren umma ba abinda take sai
addu,ah akan Allah ya warware kullun da amarya tayi akan
mijinta da kuma allah ya dawo mata da babban danta
Mujaheed daga N.D.A lafiya su Hafsat da Aliyu suka iso gate
din gidan suka shigo kai tsaye domin alhaji ya sanarwa da
mai gadi zuwansu, kana ganinsu kaga marasa tarbiyya,
sukayi karo da Ni Alokacin ina kokarin fitowa daga gida’
Hafsat ce tace kai makahon inane kanaji kana buge
mutane? Duk da baisan gurinwa zasu ba sai nace Allah
yabaki hakuri, Hafsat taja wani dogon tsaki banza
mahaukaci, Naji xafin kalmar sosai dan haka banyi wata-
wata ba na daga hannu na sharara mata mari, ta kwalla
wata kara ta tilasta umma da amarya fitowa aguje,suna
zuwa suka taradda da abinda ya faru, umma ta tambaye ni
Tace Abdulrazaq me ya faru na kwashe kaf abinda ya faru


Nafada mata, amarya tace sam bazata yarda ba nan take
dauko waya takira alhaji tace masa yai sauri yazo gida ba
lapiya, ba’a dade ba sai ga alhaji yadawo, Ya taramu gaba
dayanmu mutanen gidan, alhaji yafara magana kamar
haka:- Kai dai wannan yaro anyi dan iskan yaro,

yanzu ace kadaga hannu kamari kanwar amarya kuma kayi
tunanin zan kyaleka to wallahi baka isa ba don haka ko ka
tattara kayanka kabar gidan nan ko kuma ita uwar taka ta
bar gidan, agigice umma tajuyo ta zaro idanu tace alhaji
kasan me kake fada kuwa? abba yace ke kina nufin kice ni
mahaukaci ne to abinda kunnenki yaji shi nafada, dan
haka ku tashi ku bani guri, amarya da kannan ta suka tashi
suna dariyar mugunta, alhaji ma yatashi yabisu, Ni kuwa
tuni na dauko jakar kayana abinka da mai xuciya, umma
da Kanwata Phateema suka rike ni suna kuka, nima hawayen
bakin ciki suka fara zarya


a idanuna, Phateema kuka take kamar ranta zai fita Nayo waje
nakama hanya batare da sanin inda zani ba, Umma da
Phateema suna xaune suna ta rusa kuka, wayar umma ta fara
ringtone Phateema ce ta duba wayar yayanmu Mujaheed ne yake
kira cikin hanxari ta daga tana shashshekar kuka hello!
Yaya tace, a firgice Yaya Mujaheed yace my sister lpy kike kuka??

MUHADU A PART 3

Sárkî Ñè

Ab Kudancy

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »