Bani Da Lafiya Kashi Na Sittin Da Biyar (65)

0 17

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

“Ku rika yakuce duk wani wanda yake neman baku shawarar zuwa wajan YAN BORI neman magani daga jikinki da zuciyoyinku, domin a karshe BORIN da kansa ne yake kashe ya’yanshi da duk mabiyansu ko kuma ya haukatar da su ko ya hallakar da su ya raba su da IMANINSU a karshe su amshi mummunan sakamako a wurin Ubangijinsu kowa da komai.”

Matar dai tayi murmushi sai take cewa: Maman Sultan ni fa gaskiya yanzu bazan iya zuwa wurin malamin da kike cewa ba, saboda Allah ya sa an fahimtar da ni kuma na fahimci cewa bai dace zuwa irin wuraren nan ba. Alhamdulillah.

Nan tãke Maman Sultan ta sami wuri ta zauna saboda jikinta ya yi sanyi matuka, sai cewa tayi: Wai me kike nufi ne ma tukunna?

Matar: Ai wannan bayanin nawa a fili yake, kuma ina nufin maganar da mukayi da ke a baya, to yanzu na rushe ta kuma na fasa saboda na gane cewar: Babu mai iya tabbatar da komai sai ALLAH kuma duk abinda ALLAH ya tabbatar babu wanda ya isa ya hana shi tabbatuwa. Boka, malaman tsubbu, ya bori da sauransu basu da wani ikon tabbatarwa ko rashin tabbatarwa sai ALLAH shi kadai.

Maman Sultan ta mike tsaye cikin fushi, ranta a bace take maganganu tana cewa: Mtswww zancen banza kawai! Ai dama ire-iren ku ne marasa rabo musamman ma da kika hadu da wadannan kauyawan kullum cikin Hijabi na munafurci da iyayin tsiya.

Bareerah dai tayi murmushi sai tace: Au Labeeba ba cewa kikayi za ki siyo dabino a can gurin ba ne?

Labeeba : Hakika kuwa anyi haka, kinga ma wallahy har na manta, zo muje ki raka ni mana Bareerah.

Itama matar tace : Ai ni ma kam zan bi ku gaskiya saboda ku ne kuka cancanci ayi abota da ku saboda neman Rahamar ALLAH da kaucewa fushin Allah da kuma samun tsira daga AzabarSA.

Bareerah: Masha Allah, muna godiya da irin wannan kyautata zaton da kikayi mana , kuma muna kara rokon Allah ya tabbatar da abinda kike cewa kanmu kuma yasa mu gudu tare mu tsira tare.

Suka tafi suka bar Maman Sultan a tsaye a wurin, ta kasa cewa komai sai kallonsu kawai take yi, har suka bace mata bata daina kallon hanyar da suka bi ba, saboda gwiwarta ta yi sanyi matukar sanyi.

A kan hanyarsu ne sai suka ga an kafe wata sanarwar gagarumar Muhadara mai taken : “TA YAYA ZA MU KARE YARANMU DAGA SHARRIN MASU KAMBUN-BAKA DA HASSADA?”

(Insha Allah a rubutu na gaba za muji ci gaban rubutun.)

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »