Ingantacciyar Kariya Daga Shaidanu

0 104

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Matukar Zuciya ta tsarkaka to tabbas dukkanin sassan jiki ma za su tsarkaka, idan kuwa sassan jiki suka tsarkaka sai kaga babu wata kafa ko kofar da Mugayen Shedanun Aljanu da na mutane za su iya samun sararin kusantarka balle har su iya cutar da kai ta waje, ko su iya samun damar shiga cikin jikinka balle har su iya cutar da kai ta cikin jikinka.

MAFITA

Ka tsarkake zuciyarka da yawaita yin ISTIGFAARI da kuma ingantacce kuma tabbataccen Zikirin Allah a dukkanin lokutan da suka inganta arika yinsu cikin shari’ar Allah da ManzonSA Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama.

Daga cikin Azkaar din shi ne fadin wannan Addu’ar sau 100 a kullum da:

” لا إله إلا الله وحده لا شريك له، له المُلْك، وله الحمد، وهو على كل شيء قدير، “

“Laa Ilaaha Illallahu wahadahu laa shareeka lahu, lahul mulku, walahul hamdu, wa huwa alaa kulli shai’in qadeer.”

Kamar yadda ya tabbata a Hadisin Abu Huraira (ALLAH yakara masa yarda) wanda yake cikin Sahih Albukhary da Sahih Muslim, cewa: “Duk wanda ya fadi (wannan Addu’ar) a rana sau dari (100), Ya yi daidai da wanda ya ‘yanta baayi guda goma (10), kuma za a rubuta masa kyakkyawan aiki guda 100, kuma za a share masa mummunan aiki guda 100, kuma a ranar za a kare shi daga (sharrin) Shedan har ya yammanta.”

Kar muyi kasala wajan lizimtar wannan Azkaar mai cike da tarin lada da kuma samun garkuwar da kariyar Allah mamallakin rundunar da ba wanda ya isa ya santa sai SHI kadai.

Kunsan me kuwa?

Ai ina jin ma a cikin mintuna 15 kacal za ku iya kammala wannan Azkaar din cikin yardar Allah. Kar kuyi sake ya kamata Ku rika sadaukar da mintunan ku wajan yin Azkaar din nan a kullum…

ABIN LURA

“Idan baku samu damar yi da rana ba za ku iya yi da yamma, idan baku samu damar yin 100 a zama daya ba za ku iya rarrabawa, amma dai wanda akafi so shi ne ka yi shi a zama daya kuma a farkon wuni kamar yadda IMAM ANNAWAWEEY (Allah yayi masa Rahama) yayi bayani a cikin Sharhin Littafin Saheeh Muslim.

ALLAHu A’alam.

Allah yakara tsare mana imaninmu.

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)

Domin karin bayani:
👇👇👇

Dan uwanku:
Idris M Rismawy (Abu Nu’aym)

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »