Abu Labeeba ya nunawa Ummu Labeeba irin illar dake tattare da yin abota da makobciyar su Salaha yana cewa: Wato Ummu Labeeba wannan matar fa da kika dauka a matsayin abokiyarki, idan kikayi wasa za ta iya ruguza miki ingantacciyar rayuwarki kuma ta sanya fushin Allah tabbata a kanki a karshe kuma ta tsunduma ki cikin nadamar da ba ta da amfani.
Abu Labeeba yaci gaba da cewa: Ina mai ja miki kunne akan kar in kara ganin Salaha ta shigo nan gidan, amma ni ban hana ku kurika gaisawa a matsayinku na musulmai kuma makobta ba.
Ummu Labeeba dai jikinta yayi la’asar amma bata nuna wata nadama ba a zahiri, sai cewa tayi: Na ji kuma na gode, Allah ya kyauta, zanje naci gaba da ayyukan gida…
Bayan kwana biyu sai Labeeba ta fara zuwa makaranta cikin yanayin da yayi dabam da na baya, kowa yayi mamakin yadda jikin Labeeba ya sauya haka.
Labeeba ta shige dakin karatu (Library) tana nazarin darussan da sukayi, a bayan inda take zaune akwai wata matar aure mai suna Maman Sultan ta tara wasu yan mata wadanda ba su da aure a cikin Library din sunyi da’ira kamar dai suna yin karatu.
Labeeba taji sautin wasu kalamai wadanda su dai ba karatu ba kuma ba wata shawarar da zata amfanesu a duniyarsu da lahirarsu ba, hasali ma sai dai ta kara jefa su cikin halaka da tabewa.
Kaicooo…!
“Haka wasu matan auren suke dora wasu yan mata akan wata gurbatacciyar turba, su kuma yan matan kaga sun ɗare akan turbar wasu ma har gidajen aurensu za su je da ita, a karshe kuma ta ruguza musu duk wata nutsuwa da jin dadin da ke cikin zaman aure, saboda sun riki abinda ba zai amfane su duniyarsu da lahirarsu ba.”
Labeeba dai taga ya kamata ta rufe littafin ta dakatar da nazarin da take yi, ta kasa kunne da kyau domin ta saurari abinda Maman Sultan ke kokarin fahimtar da yan matan nan.
Sai taji daya daga cikin yan matan mai suna Suhaima tana cewa: To Maman Sultan ni dai kinga saurayi na ne ina kaunarsa amma na ga shi kwatakwata hankalinsa ba a kaina yake ba, sai naji ana cewa wai ana iya shawomin kansa yazama sai abinda nace ?
Maman Sultan : Kwarai ma kuwa, ai ni ina mamakin naji yarinya budurwa irinki tana kukan wai saurayi na yimata yawo da hankali, ai akwai abubuwan da idan na karbo miki su tuni za ki mallakeshi sai abinda kikace masa ayi za ayi tun kafin ki aure shi.
Suhaima taji dadi sosai, take cewa: To Maman Sultan meye abinyi ne yanzu?
Maman Sultan: Ai dole sai munje wurin malamina tare da ke sai ki bayyana masa matsalarki, kinga sai ayi duk abinda za ayi a gaban idon ki.
Suhaima taga lallaikam ba lallai ne ita ta iya zuwa wurin malamin ba, saboda gidansu akwai tsanani, sai cewa tayi: To Maman Sultan ke kije min mana idan yaso ko ma menene kinga sai ki fadamin daga baya.
A cikinsu akwai wata kawarta mai suna Bareerah sai tace: To ke kuwa Suhaima anya za ki iya irin wannan aikin kuwa na su Maman Sultan?
Saboda nasan irin wadan nan ayyukan ba ma su sauki bane kuma ana kauce hanya, har ma wani lokacin a hana ki yin wata Ibada.
Ita kuwa Labeeba tana nan ta yi jugumm tana jin duk bandarwar da ake damawa, taga Bareerah ta burgeta kwarai da gaske saboda Jajircewarta wajan fadin gaskiya, sai ta shiga karatun zuci tana cewa:
“Wayyoo Allah na ! Ina ma ace zan samu damar zantawa da wannan baiwar ALLAH din, na tabbata zan karu da ita sosai da sosai, kuma ga shi ba damar na tsoma baki na a cikin zancensu da suke yi saboda ba da ni suke yi ba.”
Bareerah dai taga lamarin na Maman Sultan yana nema ya wuce gona da iri saboda zai iya zama rigima, sai cewa tayi: Allah yabaku hakuri, idan har bakuji dadin maganar nan ba, amma ni dai na yi nan na wuce Masallaci saboda lokacin Sallah ya qarato..
Bayan wucewar Bareerah ne sai Labeeba taga Bareerah fa ta wuce…. Sai itama ta shirya littattafanta ta bi ta a baya tana sassarfa.
Ganin yadda Labeeba ta wuce ne sai Maman Sultan tace: Ikon Allah, yoo ita kuma wannan data zauna a bayan mu kar dai ace duk tana sauraron abinda muke tattauanawa akai ba nazarin karatunta takeyi ba, saboda yanzu mutane sun lalace da munafurci…
Suhaima tace: Au wai ke kina nufin baki gane yarinyar nan bane a makarantar nan? Ai wannan yarinyar ce ta ajin su kanwata mai fama da matsalar aljanun nan.
Ita kuwa Labeeba ko sauraronsu batayi ba, tana sauri domin so take ta hadu da Bareerah su tattauna wasu bayanai da ita…
Labeeba ta hadu da Bareerah a hanyar zuwa masallaci, bayan sun gaisa ne sai Labeeba take cewa:
“Baiwar Allah ai dazu ina jin duk abinda kuke tattauanawa a dakin karatu, amma kasantuwar ba na cikin ku ne yasa ban tsoma bakina ciki ba.”
Bareerah : Allah Sarki, ai rayuwar ce wasu suna daukarta daga duniya ba inda ake tunanin zuwa, alhalin tunanin hakan kuma ba karamar halaka bace.
Labeeba: Kwarai kuwa, Allah yasa mudace, dama ina so ne mu tattauna wasu bayanai da ke, kuma yanzu na ga kamar lokacin sallah ya gabato ko?
Bareerah: Ba matsala ai da sauran lokacin sallar ma ai Insha ALLAHu, ina sauraron ki…
Suka samu wuri a natse suka zauna, sai Labeeba tace: Sunana Labeeba Mahmood, nima dalibar makarantar nan ce.
Bareerah: Masha Allah, ni kuma sunana Bareerah Idris, Nima dalibar ce.
Sai Labeeba tayiwa Bareerah bayanin matsalar da take ciki, har da wurin mai maganin da suka je, sai ta bukaci Bareerah ta bata shawara akan lalurarta tana cewa:
“Kinga saboda bayanan da naga kuna yiwa Maman Sultan ne yasa zuciyata ta nutsu da bayanan kuma nace lallaikam nima ina da bukatar na zanta da ke ko na karu da wasu shawarwari akan matsala ta.”
(Insha ALLAHu a rubutu na gaba, za muji irin shawarwarin da Bareerah ta bata)
Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.
Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.
(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.
Domin Ƙarin Bayani Game Da Darrusan Marubucin.
+2348031542026
https://t.me/Rismawymedicine
rismawy86@gmail.com