Runduna Ta Biyar Kabilar Banu Asadi.

0 331

A cikin bayanin runduna ta biyar na wata Kabila mai suna Banu Asadi, sune suke da wata mummunar al’ada ta cutar da duk wani musulmi da yabi ta kusa da garin su don haka sai labara ya zowa shugaban halitta {saw}.

Sai manzon ALLAH {saw} ya shirya Runduna ta mahaya arba’in ya bawa Ukashatu kwamandan yaki domin su je su tarwatsa shakiyancin wadannan shaidanu.

A lokacin da Ukashatu ya nufi garin waƴan nan maƙiya Allah, sai da suka kusa ƙarsawa garin sai labari yazo musu don haka sai kowanen su ya cika rigarasa da iska suka gudu suka bar garin.

Amma duk da haka Ukashatu suka shiga garin suka samu wani mutum shi kadai yana ta barci sai suka ce ya nuna musu dabobin wayannan kafirai da suka gudu suka bar garin.

Ba tare da bata lokaci ba, wannan mutum ya tashi ya fara nunawa Musulmai dukiyoyin waɗannan kafirai musulmai suka tattaro dabbobi da dukiyoyin su suka juyo dasu a mazaunin ganima kuma har Musulmai suka dawo garin madina babu abin da ya shafesu dan gane da cutar wasu kafirai koda akan hanya ne.

Anan wannan Runduna tayi nasarar tsoratar da waɗanan gayyar kafirai da suke cutar da Musulmai. Kuma ankarya tattalin arzikin su balanta na su sake samun damar cin zarfin Musulunci.

Wannan shi abin da ya faru da runduna ta biyar a takaice in ALLAH yaso zamu kawo muku Runduna ta shida. Rundunar da kafirai suka samu nasara a kan musulmai.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »