Bani Da Lafiya Kashi Na Talatin Da Tara (39)

0 20

ABIN LURA

” Kuskure ne ku rika fadawa kowa irin lalurar rashin lafiyar da ya shafi zamantakewar aurenku, saboda ba komai ne ake bayyanawa kowa ba duk kusancinku kuwa, wasu abubuwan dole ne yakasance daga ku sai ku sai dai idan ta kama dole kamar wajan likitoci domin samun mafita.”

Ummu Arqam ta fahimci hikimar da yasa Abu Arqam yaki zuwa da Abu Labeeba wajan mai maganin duk da kuwa yana zaman abokinsa, sai tace: Na’am yanzu dai kam na fahimta kuwa sosai, fatan mu dai ALLAH yasa mudace.

Abu Arqam ya amsa da cewa: Ameen ya Hayyu ya Qayyum.

Bayan da su Abu Arqam suka karasa wajan Abu Ruwaihah ne sai yabasu wurin zama suka zauna kuma suka gaisa cikin mutumtawa, sai Abu Arqam yake cewa: Mu ne wadanda Abu Labeeba yayi maka bayanin nan.

Abu Ruwaihah: Na’am kwarai kuwa ya yimin bayanin ku kuwa sosai, yanzu dai akwai wasu tambayoyin da zanyi muku ne, ananne cikin hikimar ALLAH za mu iya fahimtar inda matsalar take Insha ALLAHu.

Abu Arqam: Na’am muna sauraron ka Mallam.

Abu Ruwaihah yace: Kafin nan ina so kusan cewa ALLAH ne kaɗai ke iya bayar da kyautar haihuwa ba waninSA ba, duk yadda boka yakai, duk yadda girman mai magani yakai ba za su iya baiwa wani haihuwa ba dole sai Allah ya bayar, saboda wannan Hurumin ALLAH ne SHI Kadai babu wanda suke musharaka da shi.

Abu Arqam: Kwarai kuwa Mallam, wannan ai sanannen abu ne a zuciyoyin mu tun ba yanzu ba kuwa.

Abu Ruwaihah: Yauwa ai haka ake bukata dama. Kuma ya zama wajibi ne ku tsarkake Zuciyoyinku wajan neman maganin lalurar ku, ku rika yin taka tsantsan saboda akwai mushrikai masu hallakar da jama’a su raba ku da Imaninku gaba daya a ƙarshe kuma kuyi biyu babu, ba Imanim kuma ba haihuwar. Kuyi hattara kar neman haihuwa yakai ku JAHANNAMA. ALLAH ya kyauta.

(Insha ALLAHu za muji ci gaban wannan bayanin a rubutu nagaba)

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »