Bani Da Lafiya Kashi Na Talatin Da Takwas (38)

0 519

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

ABIN LURA

“Ya kamata mutane su fahimci cewa: Duk duniya babu wanda ya isa ya baiwa wani maganin haihuwa, sai dai yabashi maganin wata lalurar da ake tsammanin itace tayi sanadiyyar rashin samun haihuwar, shi ma maganin ba lallai bane a dace saboda waraka ta Allah ce sai ya ga damar warkar da mutum ne kadai yake iya samun lafiya, idan kuwa Allah bai baka waraka ba to babu wanda ya isa ya warkar da kai. Mu mutane bayin ALLAH ne, ba mu da hurumin komai a wannan fannin sai abinda Allah ya zartar kawai.”

Abu Labeeba: Kwarai kuwa tambayoyi dai mana, saboda ananne zai fahimci inda ake tunanin matsalar take shin Jinnul Aashiq ne ko kuma Sihiri.

Abu Arqam: To, ba matsala Insha ALLAHu, yimin kwatancen inda zan same shi, sai kaima kayi masa bayanin zuwanmu in yaso zuwa gobe Insha ALLAHu sai muzo ni da Ummu Arqam din .

A haka dai sukayi sallama kowa ya wuce, Abu Arqam yayi gida shi kuma Abu Labeeba yayi wajan Abu Ruwaihah domin ya isar da sakon su Abu Arqam din.

Washe gari ne sai su Abu Arqam da Ummu Arqam suka kama hanyar zuwa wajan Abu Ruwaihah, suna cikin tafiya ne sai Ummu Arqam tace: Wai amma dama ba tare da su Abu Labeeba za muje wurin mai maganin bane?

Abu Arqam yayi murmushi sai yabata amsa da cewa: Ai ya riga ya kammala aikinsa ya hada mu da shi mai maganin ya yi masa bayanin ga abinda ke tafe da mu nan, yanzu kuma tsakanin mu yarage da mai maganin.

Ummu Arqam: Hmmm Amma dai…

Abu Arqam: Amma dai me kuma? Wato abinda nakeso ki fahimta anan shi ne: Akwai wasu tambayoyi ne da bai kamata ace waninmu yana nan za ayi mana su ba, saboda lalurar nan kamar al’aurar mu ce kar mu rika budewa kowa komai.

(Insha ALLAHu a rubutu nagaba za muji cigaban wannan bayanin.)

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »