Tarihin Sarkin Kano Tukur (1893-1894)

0 1,384

Sarkin Kano Muhammadu Tukur (1893-1894)

Muhammadu Tukur shi ne dan Sarkin Kano Muhammadu Bello dan Sarkin Kano Ibrahim Dabo.

Baya rasuwar Sarkin Kano Muhammadu Bello a shekarar alib 1893 ba’ayi wani jinkiri ba sai Wazirin Sakkwato, Muhammadu Buhari ya nada Muhammadu Tukur ya zama sabon Sarkin Kano.

Amma kafin a nada shi din, sai da aka aika wa da Sarkin Musulmi Abdurrahaman shawara a kan cewa nadin Tukur zai iya kawo yakin cikin gida a Kano. Sarkin Musulmi Abdurrahman bai yarda ya yi aiki da wannan shawara ba.

Ga abin da Wazirin Sakkwato Muhammadu Buhari ya ce game da nada Tukur Sarkin Kano:

A lokacin da na yi niyyar barin birnin Kano bayan zamana na sati biyu, sai na ga ya kamata na je na yi sallama da Sarki wato Sarki Bello, Amma halin da na tarar da shi na rashin lafīyar sa dole ban sami ganin sa ba, sai y zamanto mini tilas na koma na ci gaba da zama a masaukina don in saurara har ya sami lafiya.

Bayan kwana daya sai Rai ya yi halinsa, Allah ya yi masa rasuwa. Daga nan, sai na yi aike wajen Sarkin Musulmi don a shaida masa cewa Sarkin Kano Muhammadu Bella ya rasu.

Bayan da dan aikena ya je ya shaida masa sai ya aiko mini da takarda cewa in nada Tukur ya gaje shi.

Saboda haka ne na aika aka kirawo Madaki lbrahim Malam wato shugaban masu zaben sarki, tare da Shamaki Sa’idu da Dan rimi Yahaya da Sallama Barde da shi Tukur kansa, sukazo sabon gida, masaukin Waziri.

Sai Buhari ya ce ga takarda da na samu daga Sakkwato, ya karanta musu umurnin Sarkin Musulmi cewa ya nada Tukur Sarki. Me kuma kuka gani? Sai Madaki Ibrahim ya ce, ai babu sauran zabe tunda yake Shehu ya yanke hukunci, to, sai ka nada Tukur a matsayin Sarki.

Waziri ya nada Tukur sarki tare da wadannan mutane ya bawa Tukur wukar yanka da takobi.

Abin da ya sa Sarkin Musulmi ya yarda a nada Tukur shi ne lokacin da yana Galadima ya yi rawar gani. Shi ne ya jagoranci rundunar mayaka tun daga Kano har Sakkwato a zamanin ubansa Sarkin Kano Mubhammadu Bello. Su suka taimaka wa Musulmi a yakin Argungu.

An tabbatar da cewa kwazon da Tukur ya nuna da iya jan daga a fagen fama suka hana Argungu ta yi nasara a kan Sakkwato. A wannan karon ne aka kashe kanin tukur wanda suke uba daya wato Ciroma Abubakar, Sarkin Musulmi ya cika wa Tukur burinsa ya nadashi Sarkin Kano.

Awannan lokaci kuwa dukkan jama’ar Kano birni da kauye, maza da mata, babba da yaro sun yi imani, babu shakka, Galadima Yusufu za’a nada Sarki.

Kamar ana ganin shi ne ya fi cancanta, musamman shi babban malami ne. Kusan wannan nadi bai sami goyon bayan mutanen Kano ba, musamman ma wasu daga cikin manyan ya yan sarautar Kano. Ana ganin Wambai Shehu da Mamman Mai Lafiya ne kawai suka yi wa Tukur mubayi’a. Wazirin Sakkwato Wanda aka yi abin a gabansa ya yi musu alkawari zai sanar da Sarkin Musulmi halin da ake ciki.

Wannan dukunkune da aka yi aka nada Sarkin Kano a boye ya sa Yusufu da yan’uwansa yin yakin Basasa inda suka kafa nasu mulkin daban a wasu kauyukan Kano suka ajiye hedikwata a Takai.

Daga nan kuma fada ya kaure tsakanin Sarkin Kano Tukur da Yusufu. A cIkin yakin cikin gida na basasa tsakanin Tukarawa da Yusufawa, a wannan lokaci Allah ya yiwa Yusufu rasuwa.

Bayan rasuwar yusufun sai aka nada kaninsa Alyu yaci gaba da jagorantar yan’ uwansa Yusufawa suka tafi Kano. Da suka kwana a Dawaki, suka aika wa Tukur su hadu a Tudun Maliki inda Tukur ya taresu suka dinga fada. Daga nan Tukur ya bar garin ya tafi Tafashiya a kasar Katsina, a nan ajalinsa ya sauka, Aliyu kuwa ya shiga gidan sarautar Kano ya zama Sarki.

Sarkin Kano Tukur bai sami yi wa masarautar Kano Komai ba saboda yakin basasa ya hanashi zama lafiya.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »