Hanyoyin Da Zaabi Don Wanke Dattin Ciki.

0 2,612

YADDA ZA’A WANKE DATTIN CIKI.

Kasancewa ciye-ciye da mukeyi a rayuwar mu ta yau da kullum, sautari mukan ci abinci da kayan kwalama iri-iri fiye da sauran halittun dake rayuwa a ban kasa. Ba wata halitta daya da take da ilmin sarrafa abinci da abin sha da sauran nau’ukan abinci kamar halittar Dan-adam. Mutum kan sarrafa abinci dangin kayan zaki kamar su:

  • Biredi,
  • Biskit,
  • cin-cin,
  • Fanke,
  • Kunun zaki,
  • juice,
  • Cake.

Dadai sauran kayan zaki na gwangwani na roba da kuma na kwalba.

Baya ga abinci dangin kayan maiko kamar irinsu :

  1. Kosai,
  2. Fanke,
  3. Dankali,
  4. Kwai,


Dadai sauran nau’ikan kayamci masu maiko.

Wadannan na daya daga cikin abubuwan dake taruwa a ciki su haifar da cinkoson kazanta domin ciki zai cushe da ababuwa daban daban ya kasance wata illa ga lafiyar ciki.

Hakan ka iya haifarda da cututtuka kmaar haka:

  1. Tashin zuciya,
  2. Kumburin ciki,
  3. Rashin iya cin abinci,
  4. Gajiya da Kasala


Dadai sauran wasu cututtuka.

Domin Magnce Wannan Matsala ta dattin ciki sai a nemi.

  • Lemun tsami
  • Apple
  • citta

YADDA ZA’A HADA

za’a tafasa ruwan zafi kamar Kofi daya madaidaici na glass sai a zuba cokali daya karami na garin ginger. Sai a matse lemun tsami daya a ciki. a zuba cokali daya babba na ruwan apple sannan a sha.

An so a sha da safe kamin a karya da mintuna a kalla talatin.A sha na rana daya zai wadatar insha Allah.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »