Tarihin Asalin Kano Da Mutanen Ta

0 1,488





Idan Ana son a nakalci tarihin kano sosai,dole sai an tabo tarhin kasar Hausa.shi kuma tarihin kasar hausa sai an leka cikin tarhin kasar sudan. Ba kuma zaka samu tarihin kasar sudan ba dole sai ka koma cikin tarihin Daulan larabawa ta Bani ummayyata da ta Bani Abbasi.har ila yau kuma da binkicen labarin wani yamutsi da yasa jama’a suka rin hijira daga tsakiyar kasar Asiya suka yiwo Yamma.


Kasar Sudan itace yankin kasar Afrika ta wajen tsakiya ,daga gabas tayi iyaka da kasar Habasha(Ethiopia) daga Arewa tayi iyaka da sahara daga kudu tayi iyaka da yankin gabar Tekun Atlantic.

SUDAN ?


Ma’anar Kalmar sudan shine baki, saboda galibi al’ummar da zaune a cikin ta masu bakar fata ne. An ce zafin kasar sudan shine yake sa su baki,duk yan kunan kasar sudan tana gaf da wani guri Wanda ake Kira Haddul Etidali” wato equator. Kasar Hausa itace yankin nan na kasar sudan Wanda ke wajen tsakiya tsakiya.Daga gabas da ita kasar Borno, daga Yamma ga kasar Dahomey( janhuriyar Benin) daga Arewa Hamadar sahara daga kudu kuma kasashen Nupe da kasashen da ake Kira middle belt.


Kasar kano tana yankin tsakiya na Arewacin kasar Hausa, daga gabas tayi iya ka da kasashen Borno da Bauchi da Yamma tayi iya ka da Katsina ,daga kudu kuma tana da iya da zariya, fuskar Arewa kano tayi iya ka da Neja. Tun daga yanzu nasa zaku fara fahintar lalle kano wajibi ne ta zama babbar Alkarya saboda itace kamar tsakiyar kasar sudan duka.


Tun da dadewa kasar Hausa da kuma sauran kasashen sudan sami adabunsu na zaman Duniya daga fuska biyu mabambanta—gabas da Yamma .sa’adda sabawa tasa jama’ar wajen mongoliya ta Asiya suka suka ringa fuskantowa Yamma – Yamma ,a hankali sai masarautar ringa kafuwa ,idan wannan ta fadi sai wata ta tashi a can gabas .


Shine daga bisani mulkin farisa (Persia) ya kafu, ya mallake kasashen gabas gaba daya.


MUHADU A CIGABAN KASHI NA BIYU



Marubuci
Tarihin kano
08027270083

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »