Amfanin Wasu Saiwoyi Ga Lafiyar Jikin Dan Adam

3 9,125
  • MA’ANAR SAIWOYI

Saiwoyi na nufin wasu jijiyoyi ne ƙananan da manya waɗanda su ke riƙe da bishiya ko tsirrai. A koda yaushe saiwoyi kan kasance ne a ƙarƙashin ƙasa amma a wani lokacin sukan fito waje ma’ana su kan turo ƙasa. A ɓangaren magungunan Hausawa na gargajiya su ma ba a barsu a baya ba, domin kuwa suna bayar da gudunmawa ta musamman wajen warkar ko kwantar da cuta a jikin Ɗan-Adam ko dabba. Wasu daga cikin saiwoyin da ake haɗa magungunan Hausawa na gargajiya sun haɗa:

Karnta:

https://www.alummarhausa.com.ng/2020/06/amfanin-wasu-sassake-ga-lafiyar-jikin-dan-adam.html
  1. SAIWAR KUKA.

Ana haƙo saiwar kuka ta ɓangaren gabas sai a jiƙa a sha tana maganin ƙarfin maza .

  1. SAIWAR ZOGALA

Ana haƙo saiwar zogala a haɗa da saiwar bini da zugu da lemon tsami da kuma barkono a jiƙa a sha, yana maganin sanyi mai kumbura jiki.

  1. SAIWAR TAFASHIYA

Mata masu ciki na amfani da saiwar tafashiya, su jiƙa su sha domin samun lafiya cikinsu.

  1. SAIWAR GAUDE

Ana haƙo saiwar Gauɗe a jiƙa a rinƙa sha, yana maganin ƙarfin jiki.

  1. SAIWAR RAWAYA

Ana jiƙa saiwar rawaya a sha, ko kuma a shanya ta bushe a daka a rinƙa soyawa da ƙwai ana ci yana maganin shawara.

  1. SAIWAR BAKIN GAGAI

Ana jiƙa saiwar baƙin gagai da kayana ƙanshi a riƙa sha maganin ƙarfin maza.

  1. SAIWAR SABARA

Ana ɗebo ko haƙo saiwar sabara da saiwar lemon tsami da ganyen tsamiya a haɗa a daka, sannan a jiƙa rinƙa sha, yana magann tamama (shawara) kamar yankan wuƙa.

  1. SAIWAR JEMA

Ana haƙon saiwar jema a wanke a zuba a randa ko ruwan sha, tana maganin mayu.

  1. SAIWAR DAYI

Ana haɗa saiwar dayi da farin goro a tauna sannan a haɗiye ruwan, tana maganin farin jinni. Bugu da ƙari idan aka tauna saiwar dayi ita kaɗai aka haɗiye ruwan maganin sammu (Makaru).

  1. SAIWAR TAFASA

Ana haƙo saiwar tafasa a dafa da jar kanwa tana maganin ciwon nono

  1. SAIWAR KUKA

Ana haƙo saiwar kuka wadda ta ratsa kan hanya, ana haɗa maganin kwarce da kuma maganin soyayya. Akan haɗa abinci da ita a ba yarinya ta ci, maganin mallakar zuciyarta domin soyayya.

Sanya lambar wayarka a akwatin dake kasa don samun sabbin shirye shiryen mu ta akwatin sakon wayarka kai tsaye.
  1. Nura says

    God bless

  2. […] MAGANIN HAUSA By Alummarhausa Last updated Jun 8, 2020  6,503 1 […]

  3. Idrees Mohammed Waziri says

    Thank God bless you, u realy help me.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »