Yadda Zaki Hada Banana Cake

0 1,423

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Banana cake, cake ne mai sauki wajen hadawa ga kuma dadin ci domin indai an maida kai wajen yadda za’a hada to nikam a wajena harma yafi normal cake dadin ci da kamshi.

ABUBUWAN DA MAI HADAWA ZATA BUKATA:

  • Ayaba 2 ko 3.
  • Kwai 1.
  • Madara 150ml.
  • Suger 80g.
  • Mai 60ml.
  • Gishiri.
  • Vanilla.
  • Baking Powder
  • Fulawa 150g.

YADDA MAI HADA BANNAN CAKE ZATA YISHI.

Da farko zaki samu banana dinki masu kyau, bamasu laushi ba saiki bare bawonta saiki yayyanka ta kanana kanana kamar yadda zaki gani a hoton dake kasa.

Yadda Zaki Yanka Ayabarki

Saiki kawo kasko kamar na suyan kwai, saiki barbada suger a ciki saiki kawo wannan Ayaba (Banana) saiki shiryata a akan suger dinan da kikasa a cikin kaskonk kamar yadda yake a hoton kasa.

Hoto

Bayan kin gama wancen matakin saiki samu dan kwananki mai kyau saiki kawo kwanki (egg) kamar daya saiki fasa a ciki sai ki kawo gishiri kadan ki zuba ki dauki Vanilla dinki ki zuba saiki samu Suger dinki ki zuba.

Saiki juyasu sosai su juyu ya zama kwaiduwar kwan nan da kuma suger da kikasa su juya sosai, saiki kawo madara dinki ki zuba a ciki saiki kawo mai dinki shima ki zuba saiki juyasu sosai su juyu da wannan ruwan kwan naki saiki kuma kawo Fulawa dinki ki zuba a ciki kici gaba da juya sai kuma Baking Powder naki shima ki zuba, zakiyi ta juyawa har saikin tabbatar ya juyu sosai wannan fulawar taki bata duddunkule a ciki ba kamar yadda zaki gani a hoton dake kasa.

Hoto

Yadda zaki Juya Kayan Hadinki Sosai

Bayan kin gama juyawa ya juyu saiki kawo wancen kasko naki da kika shirya ayabarki (Banana) saiki zuba kayan hadinki a kan ayabarki dake cikin kaskonki ki tabbatar ko ina yaji wannan kayan hadi kamar yadda zaki gani a hoton dake kasa.

Hoto

Hoto

zaki Buda Yazama Ko Ina Kayan Hadinki Ya Rufe Ayabarki

Bayan kin zuba saiki dora akan wuta kamar yadda zaki soya kwai amma shi zaki dan rufe saman kidan bashi mintuna saiki bude ki juya bayansa shima yadan samu mintuna amma karyakai mintunan farko, da zarar ya soyu zakiga yayi ja kamar yadda zaki gani a hoton dake kasa.

Hoto

Masha Allah Bannan Cake yayi sai ci kawai

Sannan Idan kuma zakiyi na siyarwa zaki iya yankashi kamar haka

hoto

Kamar Haka Zaki yankashi Kina siyatwa Manyan Mutane don yafi karfin yara

ABIN LURA:


Zaki iya yinsa don Birthday amma shi na birthday zakiyishi step-step ne ma’ana kamar da mai fadi da mabiyinsa da wani mabiyin nasa haka zakiyi tayi kamar biyar ko sama da haka, kiyi step din yayi tsayi kawai shi ake bukata kamar na normal cake.

Zaki iya tambayar abinda baki ganeba kuma.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »