Takaitaccen Tarihin Mudi Spikin

1 1,760

An haifi Alhaji Mudi Spikin a ranar 1 ga watan Oktoba 1930, a unguwar Darma da ke birnin Kano. Yayi karatun qur’ani a hannun Malam Umaru Badamagare. Bai taba zuwa makarantar boko ba, amma duk da haka, ya zauna jarrabawar GCE Ordinary level, ta hanyar yin rijista da wata kwaleji a Ingila, acikin 1960.

Ya sami illimin zamani ne a hannun abokansa na gwagwarmayar siyasa irinsu; Malam Sa’adu Zungur, Malam Aminu Kano, da kuma Alhaji Yusuf Maitama Sule.

Yana cikin mutanen da suka kafa jam’iyyar kwato yancin talaka wato NEPU a 1950. Ya fara rubuta wakokinsa tun a 1948, ya fara da wakarsa ta “Rasha Abokan Tafiya”, da kuma wani raddi da yayiwa malaminsa, wato malam Sa’adu Zungur maitaken “Arewa Jamhuriya Kawai”.

  1. Audu says

    Yayi sosai

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »