YAWAN FITAR RUWA MAI KAIKAYI DAGA FARJI

1 4,828

HANYOYIN MAGANIN INFECTION


A gwada daya daga cikin wadannan:-
1)A samu Saiwar Garafuni da Sassaken Magarya, sai a tafasa, idan ya dan huce sai mace ta dinga kama ruwa da shi. Kullum sau daya. Yana maganin budewa da kaikayi.
2) A samu Garafuni da Sassaken Sanya sai a tafasa, mace ta dinga shan rabin kofi da safe, rabi da yamma. Yana fitar da dattin mara da maganin farin ruwa mai wari.
.
3) A samu Furen Tumfafiya, sai a shanya ya bushe, a daka a dinga zubawa a cikin Nono ana sha. Yana magance matsalar ruwan infection.
.
4) A samu Lalle da Ganyen Magarya da Kanumfari, a hada waje daya a daka sannan a tafasa a zuba farin miski a ciki. Idan ya dan huce sai ta shiga ciki ta zauna tsawon kamar minti goma. Yin haka yana maganin kaikayi da kuraje da budewa da dadewar gaba.
.
5) A samu Kabewa a dafa ta, bayan an dafa sai a tsame daga ruwa a jajjagata ko a birga, a zuba Madara ko Nono sannan a sa Zuma a sha. Wannan yana mganin rashin sha’awa da bushewa da rashin gamsuwa.
.
6) A dafa Zogale, idan ya dahu sai a murje shi ko a dama, a tace, a yi lemon juice da shi. Yana maganin fitar farin ruwa mai wari da cushewar mara kuma yana kara ni’ima.
.
7) A samu `Dan-Tamburawa da Albabunaj a tafasa a zuba Man Hulba a ciki. Sai ta dan tsuguna tururin ya dinga shigarta. Idan ya dan huce kuma sai ta shiga ciki ta zauna. Zai magance mata kaikayi da kuraje kuma yana sa matsewa.
.
8)A samu Farar Albasa da Kanumfari da Citta da Malmo da Barkono da Raihatul Hubbi, sai ta dake su tay Yaji ta dinga cin abinci da shi. Yana saukar da ni’ima da magance duk
matasalolin sanyi.
.
9)A samu Sabulun Zaitun da Sabulun Habba sai a daka su. A samu ganyen Magarya da Garin Bagaruwa a daka a tankade. Sai a zuba akan sabulan da aka daka sannan a kwa6a da Ma’ul Khal, a zuba Man Tafarnuwa da Farin Almiski. Sai mace ta dinga kama ruwa da shi kullum sau daya. Da ruwan dumi amma ake tsarki da shi. Wannan Sabulu yana maganin kuraje da kaikayi da fitar wari.
.
10) A samu Man Zaitun da Man Habba da Man Tafarnuwa da Man Kanumfari sai a hadesu waje daya. Mace ta dinga shan cokali daya kullum kafin ta karya. Yana wanke dattin mara kuma yana samar da ni’ima.
.
11) A samu Ciyawar Kashe-Zaqi da Farin Magani sai ta hada waje daya ta dinga jika rabin karamin cokali tana sha. Sannan ta dinga shan Man Zaitun Cokali daya kullum kafin ta karya. Wannan yana maganin dattin mara da wanke daudar mahaifa.
12-Asamu garin saiwar Zogale se a debi cokali daya adafashi da ‘yar jan kanwa se adinga sha. Yana maganin fitar Ruwa ta gaba in sha ALLAHU ***

  1. Salim shehu says

    Gaskiya Muna godiya sosai wallahi , Sabida Matsaloli da dama Ana magancesu tanan Cikin sauki,, Sabida haka Malamai Allah yataimaka Yakara basira

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »