TAMBAYOYI DA AMSHOSHI AKAN AZUMI

0 679

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

TAMBAYA : Minene hukuncin wanda bai samu yin Azumin watan Ramadan ba saboda dalili na rashin lafiya,kuma bai samu sauKi na rashin lafiyar ba har wani wata na Ramadan ya zagayo?


AMSA: Idan Azumin watan Ramadan dukkansa ko wani sashensa ya ku~uce ma mutum saboda rashin lafiya,kuma rashin lafiyar ya cigaba har wani watan Ramadan ya zagayo,to ba wajibi bane ya rama kwanukan da suka ku~uce masa,yanzu abinda zai yi shine ciyarwa,amma da ace uzurin da ya hana ci yin Azumin wani dalili ne ba rashin lafiya ba misali kamar tafiya,kuma ya cigaba da tafiyar har wani Ramadan ya zagayo,to anan wajibine ya rama Azumin wato ba ciyarwa zai yi ba.


TAMBAYA: Minene hukuncin wanda akwai ramakon Azumin Ramadan akansa amma ba tare da wani dalili ba sai bai rama ba har wani watan Ramadan ya zagayo?
AMSA: In dai babu wani uzuri da ya hana shi ramawa,to ramuwar da kuma kaffarar jinkiri ta hau kansa,wato wajibi ne ya rama Azumin da kuma ciyarwa.


TAMBAYA: Minene hukuncin wanda mahaifinsa ko mahaifiyarsa suka rasu alhali akwai bashin Azumi ko ramakonsa akansu?


AMSA: Wajibi ga babban Da namiji shi Kashin kansa ya rama masu Azumin ko kuma ya yi jinga da wani wato ya biya shi akan ya rama masu.


TAMBAYA: Minene hukuncin yin Azumi a tafiya cikin watan Ramadan?


AMSA: Duk wanda yayi tafiya a cikin watan Ramadan in har tafiyar ta kai ga haddin yin }asaru to wajibi ne ya aje Azumi-Sai dai akwai wasu yanayoyi da koda mutum yayi tafiya ba zai aje Azumi ba misali mai kasuwanci daga wannan gari zuwa wannan gari,ko mai tu}in mota wato zuwa wasu garuruwa ko kuma ya je waje da nufin zai kwana goma ko sama da haka da dai sauransu.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »