AMFANIN WASU TSIRRAI GUDA GOMA SHA BIYU

0 3,277

Get real time updates directly on you device, subscribe now.


1 – doddoya (Scent Leaf): Wannan ganye da aka fi sa wa ko a miya ko a dafa-duka domin karin kamshin abinci, yana da matukar amfani ga lafiya. Binciken masana kayan abinci da na ganyaye da dama bai nuna illar wannan ganye ba ga lafiya, sai dai ma nuni ga alfanun da zai iya yi wa mutane masu farfadiya da hawan jini.


2 – dinya (Black Plum): Wasu ’ya’yan itatuwa ne da mukan sha a yau-da-kullum. dinya na daya daga cikin albarkatun itatuwa da Allah Ya yi mana a wannan kasa, wadda kusan muka kusa mantawa da ita. Tana da sinadaran bitaman musamman na rukunin C da ma’adinai irinsu potassium da dama, wadanda jiki kan bukata a yau da kullum. Tana da amfani wajen ware ciki kamar lemon bawo, ga wanda cikinsa ya cushe ya kasa bayan gida na tsawon kwanaki.


3 – dorawa (Honey Locust): Ita ma kayan marmari ce mai cike da amfani. Banda sinadarin fibre mai wanke ciki da tsane maikon da ke jikin hanji, an yi amanna wannan itace ’ya’yansa na da sinadarin protein irin wanda ake samu a gyada ko waken soya, wato bayan kayan marmari ke nan zai iya zama abinci.


4 – Gujiya (Bambara Nut): Wannan abinci da a da yake da yawa a kasar Hausa ta Najeriya, a yanzu wai a kasar Mali da Nijar aka fi noma shi. Kowa ya san dadi da gardin gujiya kamar na wake, amma ba ta kumbura ciki sosai kamar waken, kuma tana da gardin gyada har ila yau amma ba ta da maiko sosai kamar gyada. Kuma a kimiyyance dukan amfanin da ake samu a jikin wake da gyada, su gujiya ta hada a wuri guda. Lallai garin dadi na nesa.


5 – Goruba (Doum Palm): Wannan abinci mai cike da sinadarin fibre mai wanke cusasshen ciki da tsane maikon jiki, dusarsa kamar dusar aya amfaninsa yake, amma ya fi aya aiki. Akan iya fasa wadda ba ta nuna ba ma sosai a sha ruwanta kamar ruwan kwakwa. Masu bincike a kan wannan dan itace suna ganin idan ana cinsa za a iya rage hadarin kamuwa da ciwon hawan jini da na kiba.


6 – Kadanya (Shea): Su kuma ’ya’yan wannan itace maiko ne da su da wasu ke amfani da shi ba ma kawai a abinci ba, har da man shafawa da sabulu. Duka yawanci kayan marmari masu maiko suna da sinadaran bitaman da ake samu daga maikon ’ya’yan itatuwa, wato bitaman na rukunin A, D, E da K, dukkansu sukan hadu su gyara fata. Kai an tabbatar cewa ma wasu manya-manyan kamfanonin kayan shafe-shafen mai, man kade suke amfani da shi wajen hada mai, kamar yadda ake yi da man cocoa.


7 – Kabewa (Pumpkin): A da ba a yin miyar taushe ba tare da kabewa ba amma yanzu ’yan zamani sun rage sanya ta a miyar taushe. Ban da zaki da take kara wa miya, ita ce kadai a cikin kayan miyan da ke da sinadari mai gina jiki na protein, ga wadanda ba su samu sun sa nama ko kaza ba a miyar taushen. Bayan haka Allah Ya albarkace ta da sinadaran bitaman na rukunin A da na C. ’Ya’yan cikinta kuma wato agushi ba su da wadannan sinadaran bitaman amma suna da na protein sosai fiye da na ita kabewar da kuma sinadaran maiko irin na gyada, irin wanda jiki ya fi so.


8 – ’Ya’yan Kalaba ko Kuka (Baobab Fruit): Ko kuma ’ya’yan kuka wadanda a da ake yawan jikawa a yi lamurjensu ko kuma a rika tsotsa haka, suna da sinadarin bitaman na rukunin C kusan fiye da kowane ’ya’yan itace. A yanzu dai wasu kamfanonin yin abinci kamar masu yin zumar ‘jam’ ta biredi, sukan sa wannan kalabar a matsayin abin da zai sa danko.


9 – Kurna (Ziziphus): Binciken wasu masana a kasashen Sweden da Masar ya nuna cewa ’ya’yan kurna suna da sinadarai na ma’adinan calcium da potassium da magnesium. Yana da kyau mu ma a samu tsangayar da za ta yi bincike sosai a kanta a kasar nan. Sun kara da cewa a nan gaba suna ganin dole a yi bincike a kan yadda sukan iya kasha kwayoyin cuta da dama.


10 – Lansir (Cress): Wannan kayan lambu su kuma kusan suna da duk wani bitaman da jiki ke bukata amma na rukunin A da K da C sun fi yawa. Ga sinadarai na ma’adinai iri-iri duk a dan wannan ganye.


11 – Ridi/Kantu (Sesame Seed): Su ma wadansu ’ya’yan itatuwa ne masu matukar amfani ga lafiya. Bayan sinadaran bitaman da na ma’adinai irinsu iron, magnesium da calcium, yana da sinadarin protein mai gina jiki ga maiko kamar dai gyada, amma kusan ya fi gyada amfani saboda sinadari ko ma’adinin iron wanda jiki ke amfani da shi wajen sarrafa sabbin ’ya’yan jini.


12 – Rinji (Senna): Wannan wani ganye ne a cikin maganin da muke saya a kyamis mai sakin cusasshen ciki na dulcolad. Don haka amfaninsa yana da matukar tasiri ga masu matsalar taurin bayan gida. Sai dai idan aka yi amfani da shi da yawa zai iya sakin cikin sosai.
N.B/karin Bayani: Domin sanin amfanin kowane sinadarin bitaman da na ma’adinai ga jikinmu, a nemi rubutun can baya a kan ‘Sinadaran Bitaman.’


AMFANIN AMBAR DA KUMA WASU TSIRRAI GUDA GOMA SHA BIYU
ﻓﻮﺍﺀﺩ ﻋﻄﺮ ﻋﻨﺒﺮ ﻭﺇﺛﻨﻲ ﻋﺸﺮ ﻧﺒﺎﺕ
Ambar wani magani ne da ake samun sa daga jikin wata bishiya. Wato kamar irin farin ruwan nan dake fita daga jikin bishiya. Shi ne ake hada
shi da wasu sinadarai a samar da Ambar. Kuma ana samunsa a jikin bishiyoyi da dama.
.
.
Bayan amfanin da Ambar yake da shi wajen kiwon lafiya, haka ma yana
taimakawa wajen cututtukan jiki da na jinnu ko sihiri.
.
.
Ana iya hada Ambar da wasu magungunan kamar zuma, miski, habba,
zaitun, da dai sauransu, ayi amfani da shi don samun ingantacciyar lafiya
.
.
.
Yi amfani da Ambar kadan ka samu lafiya mai yawa da yaddar Allah.
.
.
Ana samun Anbar na gari, ana samun na ruwa, ana samun na turare, ana
samun kwa6a66e na shafawa .
.
.
Yana sanya nishadi idan aka sha kilogram daya tare da zuma cokali daya.
.
.
Yana kara karfin hakori idan ana goge hakora da man sa.
.
.
Yana maganin cututtukan kwakwalwa idan ana shan sa tare da Man zaitun
da Habbatussaudaa.
.
.
Ga mai lalurar hauka sai adinga tofa ayoyin Ruq’yah a cikin Ambar a zuba
a ruwa a ba shi ya sha kuma a dinga yi masa hayaki da shi musamman a
hada da miski wajen hayakin.
.
.
Ciwon kai bari guda sai a hada Ambar da jan miski da Man juda a kwa6a
a dinga shafawa a kan kuma ana yin hayakin sa.
.
.
Ana amfani dashi wajen 6ata sihiri wanda mutum ya ci ko ya sha.
.
.
Masu hawan jini su sha kadan a cikin ruwa.
.
.
Don gyaran fata dajin dadin jiki sai a diga Ambar kadan a cikin ruwan wanka ay wanka da shi.
.
.
Mai son yin bacci mai dadi shi ma sai ya zuba kadan a ruwan wankansa.
.
.
Ambar yana taimakawa kwakwalwa wajen samun hutu mai dadi.
.
.
Amfani da Ambar yana kara kyautata karfin zuciya.
.
.
Masu cutar Asthma su ma Ambar yana taimaka musu idan suna amfani da shi.
.
.
Amfani da Ambar yana kara kyautata gudanawar jini a jikin mutum.
.
.
Yana kuma kara karfin jima’i ga maza da mata.
.
.
Amfani da Ambar na saukaka narkewar abinci a cikin ciki.
.
.
Yana kara soyayya tsakanin miji da mata, idan dayan su yana amfani da
shi.
.
.
Warkewar ciwo da kashe kwayoyin cuta, sai a zuba man Ambar a kan
ciwon bayan an wanke shi. To zai warke cikin sauki insha Allah.
.
.
Amma a kula.
.
Duk da amfanin Ambar kuma zai iya cutarwa .
.
Mata masu ciki su guji amfani da Ambar, musamman sha a ciki.
.
Ambar din da ba a gauraya shi da wani abu ba kamar ruwa da makamantansu,to a guji shan sa kai tsaye.
.
Ba’a sa Ambar a cikin ido.
.
A guji ajjiye shi kusa da yara.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »