TARIHIN MAKAMAN KANO ALH. ABDULLAHI SARKI IBRAHIM

0 2,394


An haifeshi a shekarar 1945. Yayi makarantar horon matakin farko a Wudil da Ungogo, sannan ya matsa zuwa Birnin Kudu Secondary School, Kana daga nan ya wuce zuwa jamiar Ahmadu Bello dake Zaria, Alh. Sarki Abdullahi Ibrahim ya halarchi makarantu da dama wadanda Suka hada da Jamiar Ife, University of Ife da wasu manyan makarantun dan samun kwarewa ta fannin ayyuka da gogewa a harkar gwamnati.

Makaman kano
Masarautar Wudil

Sarki Abdullahi Ibrahim, ya Fara aikin gwamnati a shekarar 1971 zuwa 1980 wanda yakai matsayin babban Secretary, daga nan ya koma babban Bankin Arewa har yakai ga matsayin Mataimakin Manager na gaba daya. A shekarar 1990, aka nada shi Babban Mai bada shawara ga Shugaban Qasa a Kan harkar ‘yan sanda (Police), sannan a 1992 ya zama Babban Director na Mulki a fadar Shugaban Qasar Nigeria, kuma a wannan shekarar ne aka nadashi MAKAMAN KANO Hakimin Wudil.

A shekarar 1993 aka kuma nada Makama Ibrahim II Babban Secretary na Musamman wato (Principal Private Secretary) ga Shugaban Qasa Janar Sani Abacha Wanda daga bisani aka mayar dashi Wajen Adana tattalin qasa (Ecological Fund) a matsayin Secretary na dundun dun har yakai ga lokachin barin shi Mulki a shekarar 1999.


Sarki Abdullahi Ibrahim Babban jigo ne a masarautar jahar Kano dama Arewa gaba daya wanda yake fada aji kuma ayi aiki dashi a qasar gaba days dama yankin Arewa gaba daya.

Insha Allah, Zan cigaba…

Marubucuci: Malam RANGER

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »