YADDA AKE GUDANAR DA BIKIN TAKUTAHA A KANO 2

0 327

Wannan shine cigaban bikin takutaha a Kano na 2

YADDA AKE GUDANAR DA BIKIN TAKUTAHA


Haqiqa kowane irin al’amari, akwai yadda ake tsara shi kuma a gudanar da shi. Don haka, kowane irin biki a qasar Hausa akwai yadda ake gabatar da shi, wannan ya hada da yadda ake tsattsara shi daki-daki da kuma irin dokokin da suke tafiyar da shi idan akwai.

Bikin takutaha ya qunshi dukkan abubuwan da ake gabatarwa a wannan rana, kama daga karatuttuka da nuna murna ta hanyar nishadi da kuma ziyarce-ziyarcen ‘yan’uwa da abokan arziki. Don haka, matakan gabatar da wannan biki su ne kamar haka:

KARATUN TAKUTAHA


A ranar takutaha haqiqa ana gabatar da karatuttuka daban-daban. Tun da sassafe malamai kan taru a cikin masallacin Madabo domin gabatar da wannan karatu.

Daga cikin karatuttukan da ake gabatarwa akwai waqoqin yabon Annabi salallahu alaihi wasallam. Yawancin wannan waqoqi ana gabatar da su ne da harshen Larabci.

Waqar da aka fi karantawa ita ce, Ishiriniya, sannan akwai kari na musamman wanda sai dan Madabo ne ya iya shi. Haka kuma, a cikin baitukan ishiriniyar, kowane gida a Madabo suna da baitinsu wanda suka zaba suka nuna sha’awarsu a kai. Don haka, a duk lokacin da aka zo wannan baiti, akan yi wa shugaban wannan gidan addu’a don tunawa da shi (Hira da M.A.M,11-12-2008).

A duk lokacin da ake gabatar da karatun takutaha, ana ganin abubuwan ta’ajibi, domin akwai wani baiti na ishiriniya wanda da zarar an zo wurin, kowa yana miqewa tsaye, domin malamai sun ce, Manzon Allah salallahu alaihi wasallam yana halartar wurin.

A wannan lokaci kuma, takardun ishiriniyar da ke hannun masu karatun, sukan tashi sama suna yawo a kan mutane. Haka kuma, makaru da ke jingine a masallacin kan rabu da qasa su dan yi sama (Hassan, 1998:95).

Bayan karatun ishiriniya, ana gabatar da wasu waqoqin yabon Annabi salallahu alaihi wasallam cikin Larabci kamar haka:

  • Kasidar isma’uli


Isma’uni aqul ya jami’i, ahlul aqul
Wa madahu hazar Rasul haira min yamdahu Muhammad
Marhaba shahru atana wulida fiha Nabina”

  • Fassarar Hausa

“ku saurare ni zan ambata ya jama’a ma’abota ambatoYabon wannan Annabi shi ne fiyayyen yabo na Annabi MuhammaduMarhaba da watan da ya zo mana A cikinsa ne aka haifi Annabinmu”.

  • Kasidar Muqamul lada

Muqamul lada sudratul muntaha Li Ahmadu la shakka fi Mustapha Muqamun wa tallahi ma misluhu Fa wahyun Ilaihi shadidil quwa

Lam kallamal Lahu Musa ala Hamdan la shakka lil Mustapha
Wa’inna Nabiyyin Abil Qasimu Habibur risalati fauqas sama

  • Fassarar Hausa

Muqami mafifici wato sudratul muntaha Ga Ahmadu babu shakka tare da Al-Mustapha Wallahi babu wani muqami ya wannan wahayi ne daga Allah mai cikakken mulki.

Annabi Musa ya yi magana da Allah godiya, babu shakka ga Al-Mustapha
Haqiqa Annabi baban Alqasim Masoyin saqo daga Allah.

  • Kasidar Ahlan bi shahril Maulidi


“Ahlan bi shahrul Maulidi Shahrul Nabiy Muhammadi
Huwa bi sa’adil as’adi Khairil Wara Muhammadi”

  • Fassarar Hausa


Marhaba da watan Maulidi Watan Annabinmu Muhammadu
Shi ne Mafificin masu daukaka Mafi alhairin Al’umma Annabi Muhammadu”.

Sannan akwai sauran qasidu da dama kamar su: Qasidar iza raka’a zamanu da Rafa’atul Umuri da Asiru zunubi da dandarani da Shahrul rabi’i da sauransu.

Barar Takutaha


A ranar takutaha ana samun sadaka ta bangarori da dama. A bisa al’ada tun ana kashegari bikin, sarkin Kano yakan aika wa da babban malami qaton sa wanda za a yanka a yi sadaka. Haka kuma duk sadakar da aka kawo, ana tara ta a gaban shugaban takutaha, sannan a rarraba ta ga sauran malamai.


A lokacin da ake gabatar da wannan biki, wasu samari kan zagaya da rubutun sha fal qwarya suna bai wa mutane, suna cewa, “A sha a shafa sadaka sai an niyya”. Haka kuma wasu kan debo ruwa da qasar masallacin Madabo suna bai wa mata da yara ana ba su sadaka.


Har wa yau, a tsakanin masallacin Madabo da gidan babban malami, akan sami wasu samari, daya daga cikinsu ya yi rawani ya zauna, ana ta wanke allon sha, ana zubawa a kwatanniya, ana bai wa jama’a suna sha. Wadannan samari sukan ce wai mai nadin nan jikan babban malami ne. Jin haka, sai mata su yi ta zuwa suna ba shi sadaka yana yi musu addu’a ko tofi a cikin auduga ko kwalli. Haka kuma, akan ajiye ganyen baure a gabansa, wai na gonar babban malami ne, haka jama’a za su yi ta ba da sadaka, ana ba su ganyen bauren don neman albarka (Ibrahim,1982:288).


Haka kuma, a kan Dala ana samun masu neman sadaka, wadannan suna samun wuri ne su kame, suna jan carbi, ba sa magana da kowa, wai su waliyyai ne. Wasu samari kuwa har kogo sukan samu a kan Dala su shiga ciki, yara su yi ta leqawa, suna kallonsu, suna ba da sadaka. Baya ga haka, akwai barar takutaha da yara da samari kan tafi zuwa kasuwar kurmi, wadansu kuwa datse hanyoyin cikin gari suna barar (Yahaya da wasu,1992:104).

“Takutaha bara muke
Amshi: takutaha sadaka
Takutaha ta Annabi
Amshi: takutaha sadaka
Takutaha yau sallah
Amshi: takutaha sadaka
Takutaha mai gero
Amshi: takutaha sadaka
Takutaha mai dawa
Amshi: takutaha sadaka
Takutaha mai takalmi
Amshi: takutaha sadaka
Takutaha mai zanna
Amshi: takutaha sadaka
Takutaha mai mota
Amshi: takutaha sadaka
Takutaha mai keke
Amshi: takutaha sadaka
Takutaha daga wannan
Amshi: takutaha sadaka
Takutaha daga wannan
Amshi: Sai ta badi sadaka
Takutaha Allah karba
Amshi: takutaha sadaka
(Yahaya,1979:244)

Baya ga wannan salon barar takutaha, akwai kuma malaman makarantu da suke tsayawa a kan hanyoyi da almajiransu suna rera irin wannan waqen;

“Me taka so aljanna me taka so
Amshi: Sadaka
Me taka qi aljanna me taka qi
Amshi: Rowa
dan gero aljanna dan gero
Amshi: Sadaka
‘Yar dawa aljanna ‘yar dawa
Amshi: Sadaka
Me taka qi aljanna me taka qi
Amshi: Rowa


Haka ake ci gaba da barar takutaha bayan gama karatu a Madabo, har kusan rana ta fadi.

Tijjani Shehu Almajir
Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya,
Jami’ar Bayero, Kano.

Masha Allah A nan zamu tsaya sai a kasance damu a na Uku (((((((3)))))))

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »