TASIRIN ADDININ GARGAJIYA DA HANYOYIN YADA LABARAI NA HAUSAWA

0 868

Daga Garkuwar Tarihi

TASIRIN ADDININ GARGAJIYA

A halin da ake ciki yanzu, ko da yake mafi yawan Hausawa sun karbi addinin musulunci hannu bibiyu, har ma ta kai fagen da an ambaci sunan Bahaushe sai a kawo addinin musulunci ciki, don ganin cewa Hausa da musulunci sun kusa zama abu daya duk da haka akwai Hausawa wadanda har yanzu tasirin addinin gargajiya bai bar su ba.

Sanin kowa ne cewa har yanzu akwai Maguzawa a kasashen Kano da Katsina wadanda ba su daina yin tsafi da bautar gumaka ba. Wadannan Maguzawa har yanzu sukan yi bukukuwa da tsafe-tsafe iri-iri.


Ta hanyarsu ne wasu Hausawan musulmi kan nemi taimako wajen dodo don neman biyan bukata. Irin wannan da’awa ta sa na sami wani tsohon Bamaguje a Jammawa ta kasar Dawakin Tofa wanda ake kira Zuga don ya tabbatar min ko Hausawa musulmi sukan nemi taimako a wurinsu, Zuga ya bayya min cewa a matsayinsa na makeri, ya sha karbar ziyarar makera Hausawa kuma musulmi wadanda suke zuwa wajensa don neman taimako kan yadda za su sarrafa wuta.

Ya ce yakan fayyace musu fa lallai sai an kauce kuma sun yarda suna kuma bin dukan abin da ya nuna musu na game da tsafi. Haka kuma na sadu da wani dattijo a wani kauye mai suna Katsardawa ita ma a kasar Dawakin Tofa take. Shi wannan Bamaguje sunansa Girbau kuma gawurtaccen manomi ne, ya bayyana min cewa ya ba mutane da yawa Hausawa kuma musulmi asirin dodo don kawai su tara hatsi da yawa. Idan muka juyo ta fannin bori (wanda al’ada ce ta Maguzawa masu bin addinin gargajiya), za mu ga cewa har kwanan gobe Hausawa musulmi suna yi kuma duk mai yi ya ba da gaskiya.

HANYOYIN YADA LABARAI NA HAUSAWA

Hanyoyin yada labarai abubuwa ne da suke tattare da kowacce al’umma, kamar yadda Hausawa kan ce ‘tun ran gini tun ran zane’. Hanyar yada labarai hanya ce tsararriya da ake bi domin isar da sako ga daidaiku ko kuma jumlar mutane ba tare da wani tarnaki ba.

Babu shakka hanyar yada labarai ta dade a cikin al’umma amma, tun tuni, mun dade a kasar Hausa muna da tsarin isar da sako ta hanyar yekuwa ko shela da sankira yake yi domin fadakarwa ko sanarwa ko kuma nusarwa ga mutane ko ilmantar da su dangane da wani muhimmin abu da ya shafi rayuwarsu. Irin wannan yekuwar (shela) tana daga cikin tushen kafafin yada labarai a kasashen Afrika, musamma ma kasar Hausa.

KAYAN SAWAR HAUSAWA

Hausawa a da can ba su da wata sutura da ta zarce warki sai kuma ganye, amma zuwan addinin musulunci kasar Hausa ya canza rayuwarsu ta hanyoyi da dama, misali, ko wajen sutura ma musulunci ya canza tsarin adon Hausawa, zuwan Larabawa da wasu kabilun Masar suka kawo wa Hausawa suturu masu rufe al’aura, kamar su riga ’yar Tambutu da jabba da Kaftani da Kubta da wanduna iri-iri da hular dara.

Aka kuma tanadar wa mata zane (gyauto) da mayafi (gyale) da dankwali da riga. Saboda samun irin wadannan suturu su ma Hausawa suka kago irin nasu suturun don maza da mata kamar ’yar-shara da taguwa da aganiya da fatari da bante. Wasu sun ce bante Hausawa sun aro shi daga wajen Nufawa ne.

Ire-iren Suturun Da Hausawa Suke Amfani Da Su Luru, Gwado-babbar kwarya da karamar kwarya Babbar riga da ’yar ciki-gari Shakwara da jamfa da wando Doguwar riga Launukan Babbar Riga Gari da Sace da Shakwara da Aganiya- akwai wadanda ake yi musu ado a ba su wasu sunaye: Kamar Aska tara mai cibiya da Aska takwas malummalun da Aska biyu mai wau da Girke da Girken Zazzau da Girken Nufe da Sace mai adda da Sace mai gafiya.


’Yar Tambutu da Doguwar riga da Fanjama da Hartin da Jallabiyya da Zuleka da Kaftani ’Yar ciki dahariya da ’Yar shara da Zuhuni da kuma Falmaran Wanduna Tsala da Fanyama da Bulus da Dan itori da Dantunis mai kamun kafa da kuma Kwarjalle.

Huluna Dankwara da Bakwala da Damanga da Habar kada da Facima da Zanna da Kube da kuma Zita Rawani Harasa da Bakin fara da Dankura da kuma Mubarrashi Takalma Dangarafai da Sambatsai da Fade da Mai gashin jimina da Dan Maroko da kuma Huffi.

Zanin Mata Saki da Bunu da Bakurde da Gam Sarki da Tsamiya da Dantofi da Fatari da Saro da kuma Mukuru Sana’o’in Hausawa Kasuwaci da Fatauci da Saka da Rini da Farauta da Jima da Noma da Kiwo da Kira da Sassaka da Dukanci da Gini da Fawa da kuma Wanzanci.

Muhalli Bukka da Tsangaya da Dakin Hayi da Shigifa ko Soro da Kudandan ko Rudu da kuma Kago.

AL’ADUN HAUSAWA

Hausawa mutane ne musu tsananin rikon al’adunsu na gargajiya, musamman wajen tufafi da abinci da al’amuran da suka shafi aure ko haihuwa ko mutuwa da sha’aninmu’amala tsakanin dangi da abokai da shugabanni da sauransu, da kuma al’amuran sana’a ko kasuwanci ko neman ilmi.Tun daga zuwan Turawa har yau, Hausawa suna cikin al’ummomin da ba su saki tufafinsu na gargajiya sun ari na baki ba. Galibin adon namiji a Hausa ba ya wuce riga gari da wando musamman tsala, da takalmi fade ko kafa-cik, da hula kube, ko dankwara, ko dara. In kuma saraki ne ko malami ko dattijo, yakan sa rawani. Adon mata kuwa, zane ne da gyauton yafawa, wato gyale da kallabi da taguwa da ’yan kunne da duwatsen wuya wato tsakiya.

Yawancin abincin Hausawa kuwa, ana yin sa da gero ko dawa ne. Sai kuma sauran abubuwan hadawa, da na marmari, kamar su wake da shinkafa da alkama da kayan rafi da sauransu.

Yawancin Hausawa Musulmi ne saboda haka yawancin al’adunsu da suka shafi aure da haihuwa da mutuwa duk sun ta’allaka ne da wannan addni, sai dan abin da ba a rasawa na daga al’adun gargajiya musamman a wajen Maguzawa.

Haka kuma wajen mu’amala da iyaye ko dangi ko abokai ko shugabanni ko makwabta ko wanin wadannan, yawanci na Musulunci ne. Haka nan sha’anin sana’a da kasuwanci da neman ilmi duk a jikin Musulunci suka rataya.

Da can, sana’a da kusuwanci da neman ilmi suna bin gado ne, wato kowa yana bin wadda ya gada kaka da kakanni. Kuma idan mai sana’a ya shiga bakon gari zai je ya sauka a gidan abokan sana’arsa ne. In ma koyo ya zo yi, zai je gidan masu sana’ar gidansu ne. Saboda haka kusan kowace sana’a akwai sarkinta da makadanta da mawakanta, kai har ma da wasu al’adu na musa yinta da suka sha bamban da na sauran jama’a.

TATTALIN ARZIKIN HAUSAWA

Kalmar tattali tana nufin kula ko ririta ko tanadi da kula ko adana wani abu, wato tsiminsa. Ita kuwa kalmar arziki a nan tana nufin tajirci ko dukiya ko samu ko hali ko gafi ko kudi ko sukuni ko daula ko wadata ko abin hannu wato mllakar dukiya mai yawa fiye da sauran abubuwan bukata.

Daga wadannan bayanai za a ga, a ma’ana ta gama-gari, tattalin arziki yana nufin kula da dukiya. A fagen nazari kuwa, tsari ne na sarrafa al’barkatun kasa da sauran ni’imomin da Allah ya yi wa mutum, yadda za a samar da muhimman abubuwa da dan’adam yake bukata a kuma sarrafa su ga jama’a.

Dangane da haka, dan’adam tilas ne ya yi aiki ya sarrafa wasu abubuwa don ya kai ga biyan wadannan bukatu, amma kuma mutum bai iya wadatar da kansa da dukkan bukatunsa, don haka dole ya dogara da ’yan’uwansa wajen samun wadannan abubuwa, kamar yadda su ma suka dogara da shi.

Tattalin arzikin Hausawa na gargajiya abu ne kara zube inda ake barin abubuwa kara zube, ma’ana kowa yana ba da gudummawa gwargwadon karfinsa kuma yana samun abubuwa gwargwadon irin sana’arsa da kwazonsa da kuma sa’arsa. Ita kuma hukuma ta sa ido don tsaron mutunci da dukiyar al’aumma.

Sana’o’i su ne mafi girman tafarkin da Hausawa suke bi don samar da abubuwan bukata. Ta hanyar sana’o’i suke sarrafa albarkatun kasa da sauran ni’imomin kuma rarar da suka samu suke musanyawa su mallaki abubuwan da ba za su iya samar wa kansu ba.

A takaice dai sana’o’i su ne kashin bayan tattalin arzikin Hausawa na gargajiya wadanda suka hada da noma da kira da wanzanci da fawa da saka da jima da dukanci da sassaka da rini da dillanci da bokanci da dibbu da dinki da magori da tuggu da kwarami da banbadanci da kuma koli da dai sauran su. Daga cikin wadannan sana’o’i noma shi gidan kowa da shi, a gargajiyance duk Bahaushe manomi ne amma kuma yakan kara da wata sana’ar don tallafawa. Dangane da haka ne ake karkasa mazauna gari bisa tsarin sana’o’in kowane gida ko unguwa, don haka ne ma a Kano aka sami unguwannin Makera da Dukawa da Mahauta da unguwar gini da makamantansu.

MANAZARTA

Adamu, Muhammad Tahar; 1997: Asalin Hausawa Da Harshensu. Kano: Dan Sarkin
Kura Publishers Ltd.


Alhassan, Habibu da Musa, Usman Ibrahim da Zarruk, Rabi’u Mohammed; 1982. Zaman
Hausawa, Bugu na Biyu: Lagos:Islamic Publications Bureau.


Adamu, Muhammad Tahar; 1997: Asalin Magungunan Hausawa Da Ire-ire-iresu. Kano:
Dan Sarkin Kura Publishers Ltd.


Dawaki, Alahassan Muhammad; 1983. Tasirin Addinin Gargajiya Kan Hausawa:
Takardar da Aka Gabatar a Taron Malamai da Dalibai na Jami’ar Bayero, Kano,
Sashen Harsunan Nijeriya.


Gidan Dabino, A.A.; 2001. Gudummawar Finafinan Hausa Game da Addini da
Al’ada: An gabatar da Wannan takarda a Bikin Makon Hausa na 23 Wanda
Kungiyar Hausa ta Jami’ar Bayero ta shirya, a Tsakanin 5 zuwa 8/1/2001.


Gusau, Sa’idu Muhammad; 1982.Wasanni Don Yara. Kano:
Jola-Ade Printers.


Gidan Dabino, A.A.; 2003. Ta Leko ta Koma: Mujallun Hausa Ina Mafita: An gabatar da Wannan Takarda a Taron Shekara-shekara na Mujallar Ar-Risala, a Harabar Makarantar Farhan, Kabuga Jan Bulo, Kano.


Magaji, Ahamad; 1986. Gudummawa a Kan Kokarin da Ake yi na Samar da Cikakken
Tarihin Hausawa: Takardar da Aka Gabatar a Taron Malamai da Dalibai na
Jami’ar Bayero, Kano, Sashen Harsunan Nijeriya

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »