TARIHIN SAMUWAR BIKI A KASAR HAUSA

0 3,809

MA’ANAR BIKI


A dunqule, biki yana da ma’ana daban-daban kamar yadda masana suka bayar;

Bargery (1934:105) ya nuna cewa, biki shi ne nuna murna a yayin aure ko taron radin suna.

CSNL(2006:46) sun bayyana biki da shagali na nuna farin ciki wajen aure ko suna ko nadin sarauta ko sallah ko al’adun gargajiya.

Tsanyawa (1983) ya ba da ma’anar biki da cewa, wani abu ne na musamman wanda a lokacinsa hankalin jama’a yake tattaruwa wajen nuna farin cikinsu da kuma yin fatan alheri ga junansu don ganin Allah Ubangiji ya kawo su wani lokacin tare da fatan Allah Ubangiji ya maimaita masu.

Awai (1995) ya bayyana biki da cewa taro ne da jama’a kan yi a wani lokaci qayadajje ko kuma duk lokacin da buqatar bayyana farin cikin al’umma ta taso.

Bukukuwan Hausawa za a iya kallonsu ta fuskoki guda uku kamar haka:

  1. Biki kafin shigowar addinin musulunci
  2. Biki bayan zuwan addinin musulunci
  3. Biki bayan zuwan Turaw

TAQAITACCEN TARIHIN SAMUWAR BIKI A QASAR HAUSA

Biki abu ne mai dadadden tarihi a wajen al’ummar Hausawa wanda da wuya a ce ga lokacin da aka fara shi, sai dai tarihin ya nuna cewa, Hausawa sun fara aiwatar da biki ne tun a zamanin farko, ma’ana, lokacin da Bahaushe bai hadu da wata al’umma ba. Wannan ya samo asali daga dabi’ar dan’adam ta son sararawa da bauta wa abin da ya shallake tunaninsa ko saninsa.

Mutane kan bauta wa rana ko wata ko kogi ko duwatsu da sauransu. A sakamakon bauta wa wadannnan abubuwan, sukan taru don gudanar da bikin bauta.

Dangane da wannan, Hausawa suna da bukukuwa na gargajiya da sukan yi shekara-shekara tun kafin zuwan musulunci. Misali, bikin shan kabewa wanda ‘yan bori suke yi da bikin kalankuwa wanda samari da ‘yammata suke gudanarwa bayan an yi girbi, wannan ya shafi nishadi ne kawai.


Bayan zuwan musulunci, wasu bukukuwan sun qaru ga al’ummar Hausawa wadanda su ma yawanci akan yi su ne shekara-shekara. Su wadannan bukukuwa yawancinsu duk sun shafi addini ne ba harkar nishadi ba, domin addini ne ya kawo su. Duk da haka, sai da Bahaushe ya yi qoqarin cusa nishadi a cikinsu, kamar kade-kade da hawan sallah da sauransu.

Ire-iren wadannan bukukuwa sun hada da bikin sallar idi da na mauludi da na saukar alqur’ani da sauransu.

Harwayau, zuwan Turawa qasar Hausa ya qara samar wa da al’ummar Hausawa sababbin nau’o’in bukukuwa wadanda a yau za a iya kallonsu a matsayin bukukuwan Hausawa.

Misalin irin wadannan bukukuwa sun hada da bikin nunin amfanin gona da bikin rantsar da shugabanni da na murnar samun ‘yanci da na murnar cika wasu adadin shekaru da sauransu.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »