SIGOGIN WAQOQIN SHANTU DA TASIRINSU A RAYUWAR HAUSAWA

0 912

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

3.4.1 ADANA ALADUN HAUSAWA

Waqoqin shantu suna taka muhimmiyar rawa wajen qunshe aladu, wato babbar taska ce maadanar dabiu da aladun Hausawa ta yadda ba za su bace ba. Ga misali idan muka dauki wannan diya.

Mai gida sawo tattasai sawo tumatur
mai gida sawo barkono sawo kabewa.

Wadannan diyoyi suna qunshe da aladar hausawa ta nuna ikon mai gida da irin nauyin da yake dauka a gidansa, ta hanyar nuna shi ne ke da alhakin sayo kayan abinci da sauransu.

Sannan idan aka dubi wadannan diyan waqa za a ga qunshe suke da sanaoin Hausawa na gargajiya wato:

Jagora: santilo baqin barawo hannu kamar lauje.
Yan amshi: Dan ta ni fatu su qare na auri majemi
Yan amshi: Dan ta ni gero ya qare na auri manomi
Yan amshi: Dan ta ni kifi ya qare na auri dan su ni
Yan amshi: Dan ta ni wuqa ta qare na auri maqeri
Yan amshi: Dan ta ni nama ya qare na auri mahauci.

3.4.2 BUNQASA TUNANI DA KYAUTATA SHI

Waqoqin shantu suna bunqasa tunani da kyautata shi ta hanyar kaifafa qwaqwalwa yadda za ta bunqasa, ta iya riqe sunayen abubuwa da siffofinsu. Misali:

A ba maza niqan tsakuwa
Ba ma na tsaki ba.

A nan yara za su iya tantance cewa akwai hanya da ake amfani da ita wajen samar da tsaki, wato niqa. Haka kuma a kan sami wasu kalmomi da suke baqi a cikin waqoqin shantu wadanda masu sauraro, ko da ba su je makaranta ba za su san su. Misali:

Lalala foreber and eber real one
Ga shi star ga shi ocean,

3.4.3 DAIDAITA TSAKANIN JAMAA

Waqoqin shantu suna da muhimmanci wajen daidaita tsakanin jamaa, musamman mabambanta matsayi dangane da mallakar abin duniya. Waqoqin shantu na da hikimar tausasa zuciya, ta saduda. Ta haka sai mai akwai ya rage dagawa, marar akwai kuma, ya qara haquri, ya sami qanaa. Misali:

Jagora: Ko ba za ku ba mu ya a garin ba? Yan amshi: Mu je Tudun Wada mu yi aure Yan amshi: Yan matan Tudun Wada biyu ahu Yan amshi: In ka matsa a sa maka gyara.

Wadannan diyoyi suna nuni da daidai ruwa daidai qurji, wato kowane mutum ya tsaya a matsayinsa.

3.4.4 NUNA FASAHAR HARSHE

A cikin waqoqin shantu ana iya ganin gwaninta da fasahar harshen Hausa. Misali:

Yan amshi: Kai ka ga ido ina mai jego
Yan amshi: i kunun kanwa ya qware ta.

Wadannan diyoyi an yi amfani da tamka, ta hanyar amfani da kalma ta i. Sannan a cikin wannan diya.

Jagora: Hankaki ku ci tabo
Yan amshi: Shinkafa ta sarki ce
Yan amshi: Alkama ta Bature ce.

A cikin wadannan diyoyi an yi alamci ne da tabo inda ake nufi abinci, sannan aka yi da Hankaki ana nufin talakawa.

3.4.5 ADANA TARIHI

Waqoqin shantu suna da muhimmanci wajen adana tarihin Hausawa. Misali idan aka dubi wadannan diyoyi.

Jagora: Aliyu raba gardama
Yan amshi: Ba kifi bane uban tafiyar namu Ali
Yan amshi: Amadu ya cane akwai wani Buzu
Yan amshi: Ba Buzu bane uban tafiyar namu ne Ali.

Wadannan diyoyi da ma waqar bakidayanta, tana nuni ne da irin gwagwarmayar sarkin Kano Alu da Damagarawa a lokacin sarkin Damagaran Ahmadu Kurendaga. Don haka waqoqin shantu qunshe suke da tarihi.

3.5 TURKE A WAQOQIN SHANTU


Yawancin waqoqin baka suna da manyan manufofi, wato a kowace waqa za a sami turke guda, wanda aka gina ta a sababiyyarsa. Haka kuma za a iya samun nauoin turke daban-daban a waqoqin baka (Gusau, 2008:371). Dangane da wannan za a iya samun nauoin turke daban-daban a waqoqin shantu kamar haka:

 • Turken soyayya
 • Turken fadakarwa
 • Turken yabo/zuga
 • Turken tarihi
 • Turken koda kai

Saduwar aladu da waqa wata hanya ce dadaddiya, kuma mai muhimmanci wadda Hausawa suka mallaka domin cusa tarbiyya ga yayansu (Yahaya, 2001:34).

Don haka, a cikin wadannan diyoyi za a iya fitar da turken tarbiyya, ta hanyar nuni da yin qwazo wajen nema da kuma hani ga zagin manya. diyoyin su ne:

Jagora: Idan kana fushi daddage ka nemi naka,
Yan amshi: Taqamar ina goyonka ka zagi babba.

3.6 SALO A WAQOQIN SHANTU

Gusau, (1985:186) ya bayyana salo a waqar baka da wata hanya da makadi kan bi wajen sarrafar da zaren tunaninsa ba tare da ya sani ba ko kuma wani lokaci a sane, tare da cim ma burinsa na isar da manzancin waqarsa. Bisa haka ya karkasa salon waqoqin baka zuwa gidaje kamar haka:

 • Adon harshe
 • Kamantawa
 • Siffantawa
 • Jinsintarwa
 • Kinaya
 • Alamtarwa
 • Qarangiya
 • Aiwatar da Harshe
 • Zaben kalmomi
 • Ginin jimloli
 • Karin harshe

Dangane da wannan, waqoqin shantu suna da salo mai dadi kuma mai sauqi. Haka nan, yawanci suna farawa ne da kada shantu wanda sautin shantung ya yi daidai da waqar da za ta biyo. Dangane da rerawa kuwa, yawanci suna rerawa ne a tare.

Sannan ana yawan maimaita diya, ko don saboda gajartar diyan waqar. Dangane da amshi, yan amshi suna maimaita gindin waqar farko da aka fara rerawa.

Haka nan, suna fara bude waqar da kada shantu yayin aiwatar da ita. Dangane da abin da ya shafi walawa a waqoqin shantu, makadan suna walawa ne ta hanyar daga murya da rangaji wani sain kuma suna jefa shantun sama suna cafewa.

3.7 RABE-RABEN WAQOQIN SHANTU

Idan aka dubi tsarin waqoqin shantu, za a ga cewa, za su iya kasuwa kimanin gida biyu muhimmai wato na gargajiya da kuma na zamani.

3.5.1 WAQOQIN SHANTU NA GARGAJIYA

Wannan kaso ya qunshi irin waqoqin shantu da yanmata suke yi tun kafin su cudanya da baqin aladu, wato wadanda suke na asali ne tsantsa. Misali:

3.5.2 WAQOQIN SHANTU NA ZAMANI

Cudanyar Hausawa da baqi, musamman Larabawa da Turawa an sami sababbin aladu da tsarin ilimi na addini da na zamani. Wannan ya jawo sauye-sauye da qare-qare a cikin waqoqin baka na Hausa ciki har da waqoqin shantu.

Bisa wannan dalili, yawanci kalmomin da ake amfani da su wajen gina diyoyin waqar, ana samun kalmomin Turanci kasancewa yanmata yan makarantu ne suka fi yin su.

4.0 Kammalawa

A taqaice waqoqin shantu ba qashin yar wa ba ne idan muka yi laakari da dimbin hikimomin da ke cikinsu. Sannan waqoqin qunshe suke da aladu na zamantakewar Hausawa tun kafin cudanyarsu da baqin alumma da kuma bayan haduwarsu da baqin alummu.

Baya ga haka ina ganin lokaci ya yi da gwamnatocin qasar nan, za su dage kan ganin cewa, kafafen yada labarai da muke da su, sun karkato ya zuwa nuna abubuwan da suka danganci aladun mutanen qasar nan, yadda ci gaba zai zama a kan tafarki miqaqqe.

MANAZARTA

Abraham R. C. (1946) Dictionary of the Hausa Language. London:
Hodder and Stoughton Ltd.

Bergery, G. P. (1934) A Hausa-English Dictionary and English Hausa
bocabulary. London: Odford Unibersity Press.

Brob, M. Da Baba, A. T. (1996) Dictionary of Hausa Crafts, Qamus Na
Sanaoin Hausa, Kolon: Rudiger Koppe ber lag.

Galadanci, MKM, Yahaya, I.Y. dangambo, A. Salim, B.A. Ibrahim,
M.S. (1993) Hausa Don Manyan Makarantun Sakandare 3. Lagos:
Longman Nigeria Plc.

Gusau, S. M. (1988) Waqoqin Makadan Fada:Sigoginsu da Yanaye-
yanayensu, Musamman A Qasar Sakkwato, Juzui na daya. Kundin
Digiri Na Uku. Kano: Jamiar Bayero.

Gusau, S. M. (1985) Salo da Sarrafa Harshe a Waqoqin Baka na
Hausa a Cikin Taron Qasashe na Uku Kan Harshe da Adabi da
Aladun Hausawa, Kano: CNHN, Jamiar Bayero.

Gusau, S. M. (2003) Jagoran Nazarin Waqar Baka, Kano, Benchmark
publishers limited.

Gusau, S. M. (2008) Waqoqin Baka a Qasar Hausa: Yanaye-
Yanayensu da Sigoginsu. Kano, Benchmark publishers limited.

Gusau, S. M. (ed) (1994) Fasahar Baka Kano: Sashen Koyar da
Harsuna Nijeriya, Jamiar Bayero

Kafin Hausa, A.U. (2002) Koma Baya a Waqoqin Hausa: Waqoqin
Sarauta Proceedings of the 5th Conference of Hausa Language,
Literature and Culture, CSNL. BUK.

Mustapha, A, Musa, A. (2000) Nazari Kan Waqar Baka ta Hausa,
Zariya: Gaskiya Corporations LTD.

Umar, M. B. (1987) Dangantakar Adabin Baka da Aladun Gargajiya,
Kano: Madabaar Kamfanin Triumph

Umar, M. B. (1980) Nazarin Waqoqin Hausa, Zaria: Hausa
Publication Centre.

Yahaya, A.B (1995) Qawancen Jigo Takanin Waqoqin Sarauta na Baka
da Rubutattun, cikin Harsunan Nijeriya No. dbIII, Kano: Cibiyar
Nazarin Harsunan Nijeriya, Jamiar Bayero.
Yahaya, A.B (2001) Dangantakar Waqa da Tarbiyyar yayan
Hausawa, cikin Harsunan Nijeriya, No. dId, Kano: Cibiyar
Nazarin Harsunan Nijeriya, Jamiar Bayero.

Yahaya, I. Y. (1980) Nazarin Kayan Kidan Hausawa da Muhallan kada
su. Takardar da aka gabatar a taron Nazari Kan Hikimomin
Waqoqin Hausa. Sakkwato, Maaikatar Kyautata Jin dadin Jamaa
da Matasa da Wasanni da Aladu.

Yahaya, I. Y. Zaria, M.A.Z. Gusau, S.M. YarAduwa, T. M. (1992)
Darussan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandare 1, Ibadan:
Unibersity Press, PLc.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »