HAUSAWA DA SADARWAR INTANET

0 238

DAGA

TIJJANI SHEHU ALMAJIR
Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya,
Jamiar Bayero, Kano.

Gabatarwa:

Wannan takarda ta yi qoqarin fito da alaqar da ke tsakanin fasahar intanet da Hausawa, ta hanyar nuna yadda ake samun bayanai a intanet da kuma bin diddigin lokacin da fasahar ta samu a qasar Hausa. Bugu da qari, takardar ta yi qoqarin bayyana yadda harshen Hausa yake yaduwa a intanet.


Baya ga haka, takardar ta yi qoqarin bayyana wasu manhajojin matambayi ba ya bata (Search Engines) da za a iya shiga domin neman bayanai kan fannonin ilimi da rayuwa, ciki har da Hausa.

MAANAR INTANET

Wannan kalma ta intanet kalma ce ta Turanci, wadda ta hada kalmomi guda biyu, wato International da kuma Network.

Tsangarwa (2006:85) ya bayyana intanet da cewa, fasahar sadarwa ce da ta hada kwamfutoci a duniyance, kuma take ba su damar musayar bayanai a tsakaninsu. Don haka Intanet ba wata kwamfuta ce guda daya ba, wato wata qungiya ce da duk wata kwamfuta take da damar shiga bayan cika wasu sharuda, domin musayar bayanai a tsakaninsu.

Shiga shafi na biyu don cigaba da karatun.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »