FARKON KAFUWAR MASARAUTUN KASAR HAUSA 1

1 918

Shekaru biliyan hudu da dubu dari biyar da arba’in ne, masana tarihi suka tabbatar da cewa, sune shekarun wannan duniya da muke ciki. Kamar yadda wani kamfani dake kasar amurka, mai bincike akan tarihi da shekaru (Radiometric dating). Kamfanin dake karkashin gwamnatin United State of Amurka (Geological survey 1997) Shine ya tabbatar da hakan a wani rahoto da ya fitar mai taken ‘Shekarun Duniya’.

Haka zalika United State Census Bureau, wata hukumace dake Amurka, mai bin diddigi da kidayar al’umma. Ta tabbatar da cewa yawan mutanen dake wannan duniya ya kai adadin biliyan bakwai, a karshan shekarar ta 2012. Kuma masana tarihi sun tabbatar da cewa,Daular Hausa, Daula ce mai tsohon tarihi. Sun tabbatar da cewa ta share sama da dubun-dubatar daruruwan shekaru da wanzuwa a doron kasa.

Kamar yadda sashan tarihi na kasar Birtaniya ya tabbatar. Kuma akwai a kalla sama da mutane miliyan dari uku da ke Magana da yaren Hausa.

Wani abin da zai kara tabbatar maka da cewa, kasar Hausa ta jima da wanzuwa a doran kasa shine; Wani rahoto na baya-bayan nan, wanda ya nuna cewa. Fir’aunan da ya yi milki zamanin Annabi Musa (AS) a kasar misira, asalinsa dan kasar kano ne, wato kasar Hausa. Binciken wanda ya gudana karkashin tawagar Farfesa Umar El-zakzaky El-kanawy. Kamar yadda yazo a cikin wata jarida mai suna ‘Kaduna Voice’ (the voice of a great people) Jaridar ta tabbatar da cewa Fir’auna Seti, wanda ya yi zamani da annabi Musa (AS). Dan asalin kasar kano ne. Kuma dama tarihi ya tabbatar da cewa shi Fir’aunan, zuwa ya yi kasar misira tare da Hamana ba a can aka haifeshiba.

Kamar yaddda daya daga cikin masana tafsiril Al-QUR’AN na wannan zamanin ya tabbatar da hakan. Muhammad Ali Shankidi, a cikin wata kafar yada labarai ta saudiya. Lokacin da yake gabatar da muhadarar sa mai taken ‘tabsirul Qur’an bil Qur’an Cewa; Lokacin da Fir’auna ya shigo kasar misira tare Da Hamana, Sai suka nemi da abasu masauki.

Amma mutanan gari basu basu ba. Sabo da dama garin suna da al’adar kin amsar baki. Hakan ya ja masu dole suka koma bayan gari gindin makabarta suka sauka a nan. Haka suka ci gaba da zama a nan, duk wa ‘yanda aka yi wa mutuwa, in sun zo zasu binne mamacinsu, sai su tayasu binnewa. A haka suka samu amsuwa Har aka basu gadin kofar gari.

Hakan yasa ake masa lakabi da suna ‘bauwaba’ Lokacin kuma dama akwai wata musiba da ta aukawa garin, ta yawan sace-sace in dare ya yi. Kuma an rasa ko su waye ke wannan aikin. Hakan yasa Fir’auna da Hamana, sukace a abasu gadin garin in dare ya yi, zasu iya maido da garin cikin amince. Haka kuwa akayi, bayan da Sarki ya amince masu da wannan bukatar.

Sai sukace to zasu sa dokar hana yawon dare, kuma sukace duk wanda suka kara gani in dare ya yi, to zasu kashe shi. Jama’a suka amince da wannan doka. Domin bayan an amince masu da hakan ne, garin ya koma cikin aminci da kwanciyar hankali. Bayan wani lokacine, sai sarki ya cewa fadawansa, ya kamata in dare ya yi, masu gadin nan sun fito, muje mu musu godiya. Lokacin da dare ya yi, sai sarki ya fito tare da wasu fadawansa, dan yiwa su Fir’auna godiya.

Koda su Fir’auna suka yi arba da sarki da fadaw, sai suka ce masu miya fito daku? Kafin suyi wata-wata, suka tasammasu har suka kashe sarki. Domin dama she Fir’auna kakkarfa ne. Mutanan gari suna shakkar sa. Washe gari Fir’auna ya nada kansa a matsayin sarki.

Hakan ya tabbatar mana da cewa, Fir’auna ba haifaffan kasar misira bane, zuwa yayi, kuma kashe sarki ya yi, ya hau mulki.

Hakan ne ya sa Farfesa Umar El-zakzaki tare da sauran wasu daga cikin tawagar bincikensa suka ce, asalinsa daga kasar Hausa ya fito. Sunyi amfanine da na’urori tare da bibiyar tarihi lokacin gudanar da binciken nasu.

Kabilar Hausa dai,kabilace dake zaune a arewa maso yammacin taraiyyar Nijeriya da kudu maso yammacin jamhuriyyar Nijar tare da wasu kasashe dake a yammacin Africa. Kabilace mai dimbin al’umma, amma kuma a al’adance mai mutukar hadaka, akalla akwai sama da mutane miliyan dari biyu a sassa daban daban da harshen yake asali a gare su. A tarihance kabilar Hausawa na tattare a salasalar birane. Hausawa dai sun sami nasarar kara fadada daularsu ne tun daga shekarun 1300’s, sa’adda suka sami nasarori da dauloli kamar su daular Mali, Songhai,Borno da kuma Fulani.

A wasu lokutan Hausawa sun sami gagarimin ikon, mulki da hadaka ta kau da baki’yan neman ruwa da tsaki,da kuma neman angizon a cikinta da kuma harkallar bayi.

Masha Allah mu kasance a Farkon Kafuwar Masarautun Kasar Hausa 2

Marubuci:

IDRIS MUHAMMAD AHMAD, AL-AZHAR UNIVERSITY CAIRO EGYPT,
                                          Idrismaryam85@gmail.com 

  1. Hassan says

    Masha Allah

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »