Hausa Sai Dan’hausa (Wasu Karin Magana Guda 100)

1 16,594

Wadannan sune karin maganar da muka zakulo muku guda 100 don haka zaku iya bamu naku wanda kuka sani.

A Daga Sama!An Yi Wa Wada Kwace.
 
 A Dauki KareRan Farauta?
 
 A Dauri KashaKo A Bata Igiya?
 
 A Aiki KareYa Aiki Wutsiya?
 
 A Amshi Kadai NeBa A Ga Mutuwa Ba.
 
 A Bakin Tsoho NeGoro Kan Tsufa.
 
 A Bakin WawaAkan Ji Magana.
 
 A Bar Dariyar Mai NomaKo Bai Sayar Ba Ya Ci Abinsa.
 
 A Bar Ganin Allura KankanuwaKarfe Ce.
 
 A Bar KazaCikin Gashinta.
 
 A Bari Ya HuceShi Kan Kawo Rabon Wani.
 
 A Ci A ShaA Rage Don Gobe.
 
 A Ci Ba A Sayar BaKwai Ya Fi Doki.
 
 A Ci Yau A Ci GobeShi Ne Ci.
 
 A Cikin IdoAke Tsawurya.
 
 A Haifi Da Da SamuYa Fi A Mutu A Bar Masa Gado.
 
 A Ja Mu A Kai!An Ba Uwar Makaho Kashi.
 
 A Kashe WutaTun Tana Kankanuwa.
 
 A Lallaba A Kai TaIn Ta Fito Muna So.
 
 A Lokacin Da Mage Na NanBera Ba Ya Wasa.

A Mari MatacceDon Mai Rai Ya Ji Tsoro.
  
 A Nema A SamuArziki Ne.
  
 A Nuna Wa Na RigingineFarin Wata?
  
 A Raba Arne DaMakami.
  
 A Rabe Da Alwalar KifiA Ruwa?
  
 A Rabe Magirbin YakuwaDa Na Rama?
  
 A Rabu A GanaArziki Ne.
  
 A Rama Wa KuraAniyarta.
  
 A Rashin KiraKaren Bebe Ya Bata.
  
 A Rashin KulaAkan Kade Kudi.
  
 A Rashin SaniBako Ya Sha Ruwan Wanka.
  
 A Rika SaraAna Duban Bakin Gatari.
  
 A Sa A BakaYa Fi A Rataya.
  
 A San MutumA San Cinikinsa.
  
 A Sayar A FadiKarin Wayo.
  
 A Shekara Saran RuwaSai Tambatse.
  
 A So KareHar Jelarsa.
  
 A So UwaA So ‘Ya’yanta.
  
 A Tauna TsakuwaDon Aya Ta Ji Tsoro.
  
 A Taya Allah KiwoYa Fi Allah Na Nan.

 A Yi A GamaYa Fi Gobe A Karasa.
 
 A Yi Abin Da Za A Yi!Mahaukaci Ya Dauki Rigar Kurma.
 
 A Yi MazaA Fidda Jaki Daga Duma.
 
 A Yi Wadda Za A Yi!Bera Ya Zubda Garin Kyanwa.
 
 A Zaba A GasaTa Hana Yaro Suna.
 
 A Zuba Wa UnguluKwan Zabuwa?
 
 Abin Kwarai Ya Saba Bacewa An DanganaBa Takalmi Ba.
 
 Abin Al’ajabi!Ango Ya Kwanada Kunzugu.
 
 Abin AljihuNa Mai Riga Ne.
 
 Abin Allah!Budurwa Da Ciki; Gwauro Da Yaye.
 
 Abin Allah!Budurwa Da Jika.
 
 Abin AllahNa Annabi Ne.
 
 Abin AroBa Ya Ado.
 
 Abin AroBai Rufe Katara.
 
 Abin Ba Zai Yiyu BaAuren Mage Da Bera.
 
 Abin Ba’a Ne?An Ce Da Kare Mai Sunan Maza.
 
 Abin BanzaHanci Ba Kafa.
 
 Abin BikiNa Biki Ne.
 
 Abin Cikin KwaiYa Fi Kwai Dadi.
 
 Abin Da Aka GasaShi Ya Ga Wuta.

Abin Da Aka ShukaShi Yake Tsira.
 
 Abin Da Allah Ya YiAnnabi Sai Ceto.
  
 Abin Da Babba Ya Gani Daga ZauneYaro Ko Ya Hau Rimi Ba Zai Linkaye Shi Ba.
  
 Abin Da Baki Ya DauraHannubai Iya Kwancewa.
  
 Abin Da Dama Ta JureHagun Ba Ta Jure Ba.
  
 Abin Da Kamar Wuya!Gurguwa Da Aure Nesa.
  
 Abin Da Ke Ga AmaryaShi Takan Ba Ango.
  
 Abin Da Ke Gidan SarkiAkwai Shi A Kasuwa.
  
 Abin Da Ke Gidan SarkiAkwai Shi A Kasuwa.
  
 Abin Da KunyaUwar ‘Ya Ta Cinye Suruki Ran Aure.
  
 Abin Da Mutum Ya ShukaShizai Girba.
  
 Abin Da Ruwan Zafi Ya DafaIn Aka Hakura Ruwan Sanyi Ma Ya Dafa.
  
 Abin Da Wancan Ya Ce Shi Na Ce!Kirarin Mai Tsoro.
  
 Abin Da Ya Ba Ka TsoroWataran Shi Zai Ba Ka Tausayi.
  
 Abin Da Ya Ci DomaBa Ya Barin Awai.
  
 Abin Da Ya Ci UnguluBa Ya Barin Shaho.
  
 Abin Da Ya Dami MutumDa Shi Yake Mafarki.
  
 Abin Da Ya Kewaye GidaGidan Zai Shiga.
  
 Abin Da Ya Kora Bera WutaYa Fi Wutar Zafi.
  
 Abin Da Ya Taba HanciIdo Saiya Yi Ruwa.

Abin Da Ya ZoShi Ake Yayi.
 
 Abin Daga Allah Yake!Matar Takaba Ta Yi Ciki.
 
 Abin Dariya!Yara Sun Tsinci Hakori.
 
 Abin Duniya Mene Ne?Kaza Ta Jawo Muzuru Kwanan Gida.
 
 Abin Duniya Mene Ne?Sarkinfawa Da Kyautar Kaho.
 
 Abin FadaNa Mai Baki Ne.
 
 Abin MajinyaciNa Mai Magani Ne.
 
 Abin Mamaki!Ciyawa Da Cin Doki.
 
 Abin Mamaki!Kare Da Tallan Tsire.
 
 Abin Mamaki!Kurege Da Fada Wa Zomo Dadin Kanzo.
 
 Abin MutumAbin Wasansa.
 
 Abin Na Yi Ne!An Biya Wa Zawara Hajji.
 
 Abin Nema Ya Samu!Matar Falke Ta Haifi Jaki.
 
 Abin Sai Ido!Bebiya Ta Auri Makadi.
 
 Abin ShanyaBa A Hana Rana.
 
 Abin Su Na ‘Yan DangiBare Ina Ruwanka?
 
 Abin Tsana!Amarya A Kan Kare.
 
 Abin Tsoro!Kura A Rumbu.
 
 Abin Wani Da WuyaNemi Naka.
 
 Abin WaniBai Yi Wa Wani Magani.
 
 Abin Ya Zo DaidaiMai Ido Daya Ta Leka Buta. (Butabuta)
 
  



Ku kawo mana naku karin maganar wanda kuka sani

  1. Tamiflu says

    Salon magana kuwa kamar a ce azanci kawai, akwai hikima a maganar amma ba ta zuwa da salo irin na Karin magana,kamar a Zaurance “Yazadazo ma’ana yazo kenan, a na sassarka wasu gabobi na kalma ne dan isar da sakon da salo, wani misalin shi ne sadannidu wato sannu kenan ko wani misalin ana iya daukar kalmar farko a maida ta karshe misali likaco wato cokali da dai sauransu.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »