TARIHIN SARKIN KANO BELLO (1882)

0 1,140

Sarkin Musulmi Umar Dan Aliyu ya nada shi Sarkin Kano a Dhi al-Qa’da 1299 AH wanda yay dai dai da Satumba 1882.

Ance shi Sarkin Kano Bello ya kasance mutum ne mai yawan ilmin Addinin Musulunci da kuma yawan rokon ALLAH, har ance baya yin bacci sosai da daddare, sai dai yayi ta rokon ALLAH akan ya bashi nasara a mulkin sa. Kuma shi Sarkin Kano Bello ance baya fita yaki, sai dai ya wakilta babban dan sa wato Galadiman Kano Tukur domin ya jagoranci rundunar mayakan Kano.

Sarkin Kano Bello ya kasance mai kyauta  da  karamci ga mukarrabansa kamar yadda ake tsammanin kowane mai mulki yayi,  Mallam Muhammad Amin da Alkali Baffa Bagyane suna daga cikin manyan masu amfana da wannan karamci.

 Ya goyi bayan makarantu da Malaman ilimin addini  da yawa ta hanyar. Taimakawarsa ba ta iyakance ga Kano kawai ba saboda ya ba da gudummawa sosai ga Sakkwato fiye da magabatan sa. Ya kasance mai biyayya ga gwamnatin tsakiya ta Sakkwato har ma ya nemi shawararsu kan batutuwa masu muhimmanci. Ya kasance mai biyayya ga Sakkwato ne saboda muradinsa na dan sa Galadima Tukur.

Ya rasu a ranar Asabar 16 ga Jumada Awwal 1311 AH wanda yay dai dai da 25th ga Nuwamba 1893 a Kano, an kuma binne shi a kabarin Gidan Rumfa inda  aka binne mahaifinsa Ibrahim Dabo.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »