TARIHIN ALIYU MAI BARNO

6 4,795

An haifi Mallam Aliyu Mai Bornu ne a shekarar 1919 sannan ya fara makaranta firamari a shekarar  ta 1932. Daga baya aka koma da shi makarantar sakandare ta Yola daga nan ya tafi kwalejin Kaduna a shekarar ta 1938 sannan  ya kamala karatun sa a shekara ta  1942 bayan ya cancanci ya zama Malami Mai koyar da Ingilishi.

Mallam Mai Bornu ya koyar da Ingilishi a makarantar, Yola Middle School daga shekara ta 1942 zuwa 1946 sannan ya koma  zuwa Kwalejin Kaduna inda  yaci gaba da koyarwa a shekara ta 1954, sannan kuma ya yi aiki a matsayin Mai Kula da Gidan  Makaranta a Veterinary School  kafin nan ya tafi  zuwa Jami’ar Bristol duk dai a shekara ta 1954, don nazarin tattalin arziki (Economics).

Bayan kammala karatunsa a shekarar 1957, ya dawo Najeriya ya kuma yi aiki tare da ma’aikatar kula da jama’a ta Arewacin Najeriya a matsayin Babban Jami’in Gudanarwa inda ya rike mukamai daban-daban kafin nan yasamu zuwa Babban Bankin Najeriya a 1959 a matsayin Mataimakin Sakatare a CBN.

Mallam Mai Bornu ya ci gaba da zama Mataimakin Sakatare  kafin nada shi Mataimakin Gwamna a shekarar  ta 1962. Ya zama Gwamnan Babban Bankin farko  a shekarar ta  1963 kuma ya yi ritaya daga aikinsa a shekarar 1967.

Daga baya aka nada shi Darakta gami da  Janar Manajan Kamfanin Taba  na Najeriya wato (NTC). Kodayake ya yi murabus da nadin nasa na NTC a shekarar 1969, ya ci gaba da kasancewa mamba a kwamitin gudanarwa har zuwa rasuwarsa.

Mal Aliyu Mai Barno ya rasu   a ranar 23 ga Fabrairu, 1970.

  1. Muryar Hausa24 says

    Da kyau

  2. Arewa Boss says

    Allah ya saka da alkhairi

    1. Abdul says

      Amin Thuma A
      Min

  3. Habibu aliyu galadima says

    Allah yakara daukaka

  4. Nuruddeen says

    Allah kara daukaka

    1. alummarhausa says

      Ameen

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »