TARIHIN KAUYEN MASU GINDI DAKE KATSINA

0 2,980

MASU GINDI

Masu gindi wani kauye ne da ke karamar hukumar kafur a Jahar katsina, Karkashin masarautar Nasarawa, Kauyen sun shahara wajen yin gindin doki,wata igiya ce da ake amfani da ita wajen daure doki a kafar shi jikin turke.

Dalilin wannan yasa ake cema garin masu Gindi , Ma’ana masu yin gindin doki, Garin masu Gindi yana da da d’add’en tarihi wanda ya haura shekaru Sittin a hasashe, kasar Sabuwar kasa (Masarautar Nasarawa) sun shahara wajen yin SUGA RAWAR DOKI  (Mazan kwaila) ta dalilin haka suma masu gindi suka ba sana’ar gindin doki mahimmanci.

Kasancewar yanxu zamani ya canza  sai jamaar dake garuruwa daban daban suka sawa wannan Kauye ido kasancewar sa da wannan suna wanda jamaa da dama ke cece kuce akan cewa wannan Batsa ce wasu kuna na cewa a tarihin kenan.

Duba da yadda akasarin jamaa sukafi tattara akan cewa sunan bai dace ba don haka masu unguwani dakuma ciyaman nagarin kafur suka canzawa wannan kauye suna zuwaSABON GARIN NASARAWA.

Na dade Ina ganin hotunan mata da maza suna yawo a wannan kafa, mafi akasarin su , suna daukar hoton ne domin shegantaka, wanda yin haka shine musabbabin da yasa aka chanza ma garin suna zuwa SABON GARIN NASARAWA.

Tura Aiyukan Mu Zuwa daya daga cikin social media dake kasa Mungode

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »