Yadda Ake Gudanar Da Sana’ar Dukanci A Kasar Hausa.

0 516

MA’ANAR SANA’AR DUKANCI

Sana’ar dukanci, sana’a ce kamar sauran sana’o’in gargajiya na Hausawa. Masana sun bayyana ra’ayoyinsu game da ma’anar dukanci.

Wasu masana na ganin cewa, sana’ar dukanci, sana’a ce da ake sarrafa fata don samar da wasu muhimman kaya na amfanin yau da kullun na Hausawa. Alal misali kamar: Takalman fata, jaka, sirdin dawakai, kuben takubba, da na wuka gami da rufa Laya, Guru  da dai sauransu.

Dukanci sana’a ce da ake amfani da fatun dabbobi kamar shanu da damisa da rakumi da tumaki da barewa da gada. Haka ma ana amfani da fatun kwari kamar irin su maciji da kada da damo. Akan sarrafa fatun wasu manyan tsuntsaye kamar irin su Jimina, da Dawisu don yin mafitai da wasu kayan kawa da ake kawata jikin ginin fadar sarki ko attajirai dasu.

DUKAWA SUN KASU KASHI BIYU.

  • Akwai masu yawon neman aikin gyaran kayan fatu.  
  • Akwai na zaune wuri guda.

KAYAN AIKIN DUKANCI

kayan aikin dukanci sun hada da:

  • FATA

Fata ita ce ginshikin sana’ar dukanci, domin fata ce ake sarrafawa wajen samar da kayayyakin sana’ar dukanci ke samarwa.

  • WUKA da ALMAKASHI

Wuka da almakashi wasu abubuwa ne da dukawa ke yanka fatu a lokacin da suke aiwatar ko amfani da su don sana’arsu ta dukanci.

  • Kulki

Kulki wani ice ne da dukawa ke amfani da shi wajen bubbuga fata don ta yi yadda suke bukata a lokacin da suke son sarrafa ta, don aiwatar da wani abin bukata na rayuwar jama’a.

  • Tsinke

Tsinke shi ne karfen da dukawa ke amfani da shi wajen dunkin fata don samar da abubuwa da sana’ar dukanci ke samarwa.

  • Allura da ZARE

Allura da zare da su ne dukawa ke amfani wajen Dinke duk wani abu da suka sarrafa fata don samar da shi. A jikin allura ne ake sakala zare don samun saukin gudanar da dinkin.

  • Tuwo da Bula

Ana amfani da tuwo ko Bula wajen manne fata ko fata da wani abu da ake son hada shi da shi da fata don sarrafa su a samar da wani abin moriyar ga rayuwar Hausawa. 

Mai irin wannan sana’a ana kiransa da ” Baduku ” a kasar Hausa.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »