TARIHIN MASARAUTAR JIHAR GOMBE KASHI NA DAYA 1

0 3,547

TARIHIN MASARAUTAR JIHAR GOMBE KASHI NA DAYA

Tarihi ya nuna cikin karni na 14  aka fara sanin garin Gombe, sai dai kafin wannan lokacin an yi wasu mutane masu karama da sarauta da ake kira ‘Soninke Mandigos’, wadannan mutane su ne suka samar da tsatson garin Gombe, kuma ‘Tarekh-el-Sudan’ (mutanen yankin Sudan) ke musu lakabi da ‘Fararen Shugabanni’.      

  Wadannan mutane ana kuma kiran su da ‘Kaya- Manga’. Sun mulki yammacin Sudan na wasu karnoni da dama. A cikin Kaya-Manga an samu wani mutum da ake kira Bin- Kaya Mob, wanda sarki ne a wata masarauta da ake kira Mande, a dai yammacin Sudan din, wanda kuma wannan sarki ya ci zamaninsa a cikin karni na 10.   

      Sarki Bin-Kaya Mob yana matukar ji da jikansa Bin-Abubakar, wanda har ta kai ko kuda ba ya so ya taba shi. Ya mayar da shi dan lelensa kuma shafaffe da mansa. Hakan ce ma ta sanya Kaya Mob ya bai wa jikan nasa wani bangare na masarautar tasa da ake kira Ukuba.       

  Bin Abubakar kaka ne ga Aliyu Ukuba, wanda shi kuma yake mahaifi ga Usman. Aliyu Ukuba shahararren malami ne, ya haddace Al-kur’ani, wanda daga baya aka hada shi aure da ‘yar gidan wani attajiri a garin Tibati, inda kuma suka haifi Usman.          

Usman ya zauna a kauyen Lakumma kusa da garin Shellen, a nan kuma ya ci gaba da wa’azi don a bi addinin musulunci. Da na yi waiwaye ne kan tarihinsu game da addinin musulunci, sai na gano masarautar Kaya-Manga sun karbi musulunci daga Abubakar Almarobid (Sanha-ja-Imam) tun a shekara ta 1077, bayan Almarobid ya kafa daular musulunci a wajen.     

  Usman Ukuba ya auri Janaba ‘yar gidan Gongon (Amna), wanda shi ne sarkin Shellen. Sun haifi da namiji da aka radawa suna Abubakar a garin Mada (tsohon garin Shellen) a shekarar 1762. Zuri’ar da ake kira KAMBARIJO ke nan. Ma’anar kalmar Kambarijo ita ce zuri’a daga Kaya- Manga da kuma mutanen garin Shellen.     

  Mahaifin Abubakar ya mutu yana yada addinin musulunci a garin daga baya aka san shi da Gombe, a lokacin wajen yana karkashin masarautar Adamawa ne.            Bayan mahaifin Abubakar ya rasu ne, sai mahaifiyarsa ta mayar da shi wajen kakansa, wanda a nan ne kakan nasa ya yi masa lakabi da ‘Buba Yero’.

Kalmar Buba na nufin Abubakar yayin da Yero ta samo tsatsonta daga Kanakuru Janafalu, wanda take nufin Manyan ko dara-daran idanu.Kasancewar da ma yana da manya idanuwa.     

Sannu a hankali, sai lakabin Buba Yero ya danne asalin sunansa na Abubakar Bin- Usmanu.

Ya fara karatun Muhammadiyarsa a wajen mahaifinsa, sai dai kuma bayan rasuwar mahaifinsa, sai ya tafi Kukawa a cikin masarautar Barno, inda ya ci gaba da karatun addini.    

  A shekarar 1810 ya ziyarci mujaddadi Shehu Usman Dan Fodiyo a garin Degel. Sai dai kafin ya karasa Degel ne ya yada zango a Katsina, inda a nan sarkin Katsina ya ba shi auren ‘yarsa Zulai. An yi biki har ma Allah Ya azurta su da da namiji aka masa suna Sulaiman (sarkin Gombe na farko, 1842-1844).       

Ya sake zuwa a tarihi lokacin da Buba Yero yake zuwa Degel ya yada zango a Daura, inda a nan ma sarkin Daura ya hada shi aure da ‘yarsa Hauwa, wadda ita ce mahaifiyar Muhammadu Kwairanga (sarkin Gombe na 2).             

Tarihi ya nuna in ka dauke sarki Sulaimanu da yake da tsatso daga Katsina, sauran sarakunan Gombe tsatson masarautar Daura ne.     

  Buba Yero ya shafe shekaru goma a wajen Shehu Dan Fodiyo, wanda a shekarar 1820 Shehu ya ba shi Tuta ta 5 daga cikin tutoci 12 da ya fara rabawa.       Buba Yero ya dawo Shellen daga nan ya ci gaba da Jihadi, har lokacin da Shehu ya dakatar da shi. Daga nan kuma Shehu ya bayar da Kabilar Lala da Yungur da kuma Hona ga Modibbo Adama na Adamawa.  

Masha Allah ku kasance damu a kashi na biyu don jin yadda AKASAMU ASALIN SUNAN JIHAR GOMBE.

Tura Aiyukan Mu Zuwa daya daga cikin social media dake kasa Mungode

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »