TARIHIN MASARAUTAR GARIN MASHI TA JIHAR KATSINA

0 1,699

 

 GARIN MASHI A MASARAUTAR KATSINA

A bayanin da muka samu, an nuna cewa Mashi Tsohon gari ne Wanda ta kafu tun wajejen shekara 400, tun kafin zuwan BAKO, wato garin ya kafu tun wajen karni na 16 ke nan, amma bamu samu bayanin ko wayanne Irin mutane ne suka zauna gurin ba, amma ana kyautata zaton cewa Habe ne suka zauna gurin tunda sune suka kafa garuruwa tun kafin zuwan Fulani da Barebari da kuma wangarawa. 
To, ita dai Mashi ana iya danganta Tarihin ta da wani mutum mai suna BAKO, Wanda aka ce yazo daga kasar Maradi ko daga Daura, a wajen karshen karni na 16 kenan, saboda kasancewar Mashi kasar noma ce mai Albarka, shi ya janyo hankalin BAKO da wayanda suka biyo bayansa. 
Lokacin da wannan mutum yazo sai ya inganta harkar noma, ya kuma cigaba da tanadar makamai wato kayan yaki, Irin namu na wancan lokacin, kamar su Takobi, Mashi,  da kibiyoyi, dan tsaron garin daga mahara.
Saboda wannan Dalilin ne sai mazauna gurin suka nada shi shugabansu. Ance a duk lokacin da aka kawo wa garin na Mashi hari, idan mutane suka fito da niyyar fita yaki, zaice masu kowa ya koma gida abinsa. Shi kuma zai fita shi kadai ya kafa wani MASHI ta inda maharan suke bullowa.
 To, in dai yayi haka, ba acin garin da yaki, kai ko wucewa ba ayi ta garin matsawar MASHIN da ya kafa yana kafe, har sai inya cireshi. 
A Dalilin wannan mashin da BAKO ke kafawa ne yasa aka radawa garin sunan MASHI. Bayan zuwan BAKO, mutane sun kasance suna ta barkowa daga ko’ina suna zama Mashi domin yin noma, kasancewar gurin a kwai wadatuwar ruwan sha, kuma kasar ana samun amfani noman Gero da Dawa, Wake da Gyada da dai sauran kayan abinci. 
Da gari ya bunkasa sai akaje aka kafa Mashin Bako adai dai kofar shiga garin. A kwana a tashi gari ya bunkasa a karkashin mulkin Bako. Ganin haka sai jama’a suka dunguma suka je Katsina suka roki Sarkin wannan zamani cewa suna son idan Sarki ya amince a nada masu Bako a matsayin Sarkin su, ma’ana mai mulkin gurin. 
A kayi sa’a Sarki ya amince ya Nada Bako Sarkin nasu mai mulkin yankin. To tun daga nan ne aka rika kiran wurin da GARIN BAKO. Wanda sai daga baya ne aka koma kiran shi da Mashi.
A nan zamu iya cewa tsarin sarakunan Mashi ya fara ne daga Bako, kamar shekara 400 da suka wuce, wato wajen karni na 16. An ce Bako yayi kamar shekara 13 yana mulki. Daga Bako, bayani ya nuna cewa, Wanda ya biyo bayansa, shine 
Mashi KWANGI, Wanda yayi shekara 16 yana mulki, sai Mashi TUJA, Wanda aka Nada yanada kananan shekaru kamar 16, amma
daga baya cire shi a kayi, aka ba Mashi DUDU, Wanda Kane ne ga Mashi kwangi. 
Daga nan kuma sai Mashi DAN-WAIRE, wani jarumi mayaki Wanda yayi mulki a tsawon shekaru 3 kawai, Wanda daga baya aka maida shi Ruma. 
Daga Danwaire sai Mashi HABBARE, Wanda yayi shekara 11 a kan karaga. Daga nan sai Mashi DAURA Wanda yayi shekara 9. Wanda ya biyo bayansa shine Mashi TURARE shi kuma yayi shekara 10 cur yana mulki. 
Daga shi sai Mashi Dan Marusa Dan kawu, sai kuma Mashi DAN -GIDA, Wanda yayi shekara 15 yana mulki. To daga Mashi Dan gida ne lakabin sunan sarautar ya tashi daga mashi ya koma “IYA”. 
Iya na farko shine IYA ZAKARI Wanda yayi shekara 24 cur a kan mulki. Daga nan, sai kuma aka kawo Sarkin Gabas ABUBAKAR. bayan an dauke Abubakar an maida shi Mani, aka maye gurbinsa da IYA ABDULLAHI Wanda yayi shekara 2 yana mulki, daga shi sai DURBI UMMARU sai IYA DAN,DADA Wanda yayi shekara 4. 
Daga shi sai Sarkin Gabas IBRAHIM shekara 19, Wanda daga nan sai Sarkin Katsina Usman Nagogo ya maida shi Katsina, ya bashi sarautar IYAN KATSINA a shekara ta 1968. 
Daga nan ne sai aka ba Sarkin Gabas AMINU wato Dan Sarkin Gabas Ibrahim, sarautar iyan Mashi. Wanda kuma a 1982 aka bashi iyan Katsina kuma Hakimin Mashi. Shi kuma iya Ibrahim din sai aka bashi TALBAN KATSINA a 1982 din dai. 
Babban cikas din da muka samu game da jerin sarakunan mashi, shine babu kwanan wata da shekarun da sarakunan sukayi. Amma duk da haka jerin abin dogaro ne, abin kuma amin cewa. 
Majiyarmu ta nuna cewa a da can garin Mashi yana karkashin Dutsi ne. A lokacin sarauta gurin tana ta Magaji wadda ke karkashin Marusa, Magaji mashi. To saidai bamu samu sunan shi Dan marusan ba Wanda yayi mulkin gurin, amma ana kyautata zaton tun can lokacin mulkin Habe ne. 

Mai karatu ayi karatu lafiya idan a kwai abinda mukayi kuskure a fada mana mu Gyara saboda ajizanci na dan’adam.
Daga-Zaharadden Ibrahim Katsina

Tura Aiyukan Mu Zuwa daya daga cikin social media dake kasa Mungode

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »