TARIHIN MAI IDIRIS ALOOMA NA JIHAR BORNU

1 601

WANNAN SHINE CIKKAKEN TARIHIN MAI IDIRIS ALOAUMA KOKUMA KACE ALLOMA SARKI A DAULAR BORNU

 

 

Idiris Alooma ko kuma kace Alaoma shine “Mai” (Wato Sarkin) Bornu, Wanda yay zamani da sarauniyar Ingila Elizabeth I wato ta 1 (), 

 

Idiris Alouma jarumin gaske ne kuma sarki wanda yankin Africa dama kasashen kusa da afrika bazasu manta dashi ba a tarihi musamman yakunan Arewa, a lokacin mulikin sa alouma ya habaka yakunansa da abubuwa daban da baban, An nada masa sarautar sarki yanda shekara 25 ko 26 ya fara mulki a tsakanin shakara ta 1564.
A lokacin mulkinsa yayi kokarin ficewa daga babbn birning Ngazargamu don kafa sabuwar masarautar sa, mai nisan kilomita 5 daga kogin Yo (Komadugu Yobe) a wani wuri mai suna Gambaru, ya zagaye ganuwar garin nasa da jan tubalin kasa wanda ya yake nuna alamun mulkinsa. Wanda har yanzu zaa iya ganin wasu gine ginan a Gambaru kuma suna da tsawon mita 3.

“Mai” Tasamo asali ne daga yaren kanuri, inda mukuma muke cewa “Sarki” da hausa.

Masu bashi shawarar kan harkokin Mulkinsa sun hada da Hausa, Tuareg, Taobau da kuma Bulal wadan nan duk kabilu ne a yankin sa.
Tarihi ya nuna , cewar shine sarkin Borno na 15, yayi yakuna sama da guda dubu ɗaya a tsawon rayuwar sa ta mulki, a ciki ya samu nasara a yakuna 330 kamar yadda tarihin wasu yakunan yazo a littafin ‘Gazwatu Borno’ na marubucin sarkin mai suna Ahmad Al Furtu.
Idris Alaoma shine ya fara samarwa da dakarun yakinsa katafarrn Gurin zama wanda da zarar kazama dakaren yaki to zaa daukeka daga inda kake a kaika abaka gida a wurin ka zauna da iyalanka, Haka zalika shine wanda yafara samarwa dakarunsa hulunan sulke na karfe domin yin yaki kamar yada manyan masarautu irinsu misira da girka suka jima da yiwa dakarunsu. A lokacin Mai Idiris ya horar da dakarunsa dabarun yaki iri daban daban, wanda a cikinsu ne ya ware dakaru masu yaki a ruwa da dakaru masu yaki a kasa akan dawakai sannan ya ware masu yaki da kibiya duk suma akan dawakai.
Saboda yabawa dakuma jajircewa wajen mulkinsa ne masarautar Egypt da Ottoman suka tura dakarunsa guda 200 zuwa babbar masarautar ta Bornu ina suka keto ta cikin sahara, lokacin da Borno ke cikin birnin Ngazargamu, don kulla alaka a tsakanin masarautun guda uku wato Egypt, Ottoman da kuma Borno.
Idris Alouma shine yafara sa hannu a rubutu da akai na farko don tsagaita yaki a tsakaninsu da kasar cadi. 
Kasancewar Idris Alouma Musulmi yasanya yayi gine_gine na masalatai da kuma canza tsarin gwabnatinsa zuwa tsarin musulunci gami dayin makaratu don koyarwar addini, kuma shi yadau nauyin sanyawa a gina masaukin alhazai a saudiya saboda masu zuwa aikin haji daga barno. 
Alouma ya nuna sha’awar sa akan cinikaiya da kasuwanci da sauran alumura tattalin arziki, don haka ya samar da Jiragen Ruwa saboda manomansa su dinga fitar da kayan amfanin gonar da suka noma ta Kogin Cadi. 
Mai Idiris Alouma ya habbaka kasuwancin don kuwa har kasar Larabawa ake turawa da Goro, Silke da kuma auduga da sauran kayayaki da ake samarwa daga Daular ta Borno. Sannan ya samar da tsaro, ta inda ko a ina kake a Borno zakayi tafiyarka babu tsoran kowa babu kuma wanda zai taba kayanka. yayi yaki domin faɗaɗa masarautarsa, kuma hakika ya samu nasara gagaruma a zamaninsa. 
A zamanin mulkinsa, Daular Borno ta faɗaɗa har izuwa Fezzan ta kasar Libya daga Arewa, sannan ta shigo kasar Hausa daga Yamma, hakanan yacinye kabilun Bulala da wasu masarautu a Gabas. 
Mai Idiris Aloama ya rasu a wurin yakin da akai a Baguirmi bayan anyi masa jina-jina a gefen wani tafki mai suna Alao ko Aloo. Acan kuma akace an binneshi, don haka ake tsammanin Alooma ko alouma ya samo asali ne daga inda kabarinsa yake.
 
Tura Aiyukan Mu Zuwa daya daga cikin social media dake kasa Mungode
  1. Musa shuiabu says

    Muna godiya sosai

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »