SUNAYEN HAUSAWA NA GARGAJIYA WANDA AKE AMFANI DASU ADA

1 8,279

Jerin wasu daga cikin sunayen da Hausawan farko ke amfani da su kenan, kafin zuwan addinin musulunci kasar Hausa.
Masana tarihi sun bayyana cewa an dauki lokaci mai tsawo kafin Hausawa su dena amfani da wadannan sunayen, hatta bayan zuwan musulunci wasu sunci gaba da amfani da sunayen.
A yanzu ragowar maguzawan da suka ki karbar musulunci sune suke amfani da irin wadannan sunayen.
Sunayen Sun hadar da.

div class=”separator” style=”clear: both; text-align: justify;”>

ABARA, ABARSHI, BARAU: Ɗa namiji da ya rage bayan magajinnai nai na rasuwa.
ARZIKA: Ɗa namiji wanda uwar shi ta sha wahalar nakuda ga haihuwarshi kafin daga bisani aka haifai.
AGADA: Sa-maza-sa-mata. Namiji ko macce wadda take bi ma tagwaye.
ADARE: Ɗa namiji wanda aka haifa da dare.
AUTA: Ɗan auta a ɗaki.

ANGO: Ɗa namiji wanda aka haifa lokacinda ake shagalin aure a cikin gida.

BAKWAI: Ɗa namiji wanda yake cikon na bakwai a ɗaki.
BAKI, DUNA: Namiji wanda yakeda baki wuluk.
Bako: Namiji wanda aka haifa lokacinda aka yi baƙi a cikin gida.
BARA: Ɗa namiji na farko da aka haifa bayan magajinnai nai duk mata ne. Bara a hausa na nufin roko kenan roko shi sukai.
BAWA: Namiji wanda ya girma wajen wata macce wadda ba uwatai ba.
BABBA: Magajin wani ko wa. Namiji wanda yakeda sunan magajin wani.

BABANGIDA: Ana sa ma yaro wannan sunan in yanada suna guda da kaka a gida kuma saboda surukai suna jin kunyar faɗin suna sa, sai su laƙaba mai “BABANGIDA”, wato babbancikin gida.
ƊARI: Wanda aka haifa lokacinda ake matsanancin sanyi.
DADA: Ɗa namiji wanda uwar shi da baban shi dangin juna ne.
DANGALI: Ɗa namiji guda ɗaya tilo da aka haifa a ɗaki
DAWO, DANDAWO: Da namiji wanda aka haifa sanda uwar shi ke kirɓin dawo, abinci dangin gero da ake haɗawa tareda nono a samu Hura.
DAWI, MAIDAWA: Ɗa namiji wanda aka haifa a lokacin da baban shi ya girbe ɗarmin dawa da yawa.
GERAU, MAIGERO: Ɗa namiji wanda aka haifa lokacinda baban shi ya girbe damman hatsi da yawa.
MAIWAKE: Ɗa namiji wanda aka haifa lokacin da baban shi ya girbe wake da yawa.
SHEKARAU: Ɗa namiji wanda uwar shi ta ɗauki ciki nai tsawon shekara guda.

RUWA, ANARUWA,MAKAU, MAKAO: Ɗa namiji wanda aka haifa lokacinda ake shata ruwan sama kamar daga bakin ƙwarya a cikin gari.
HANKURAU: Namiji wanda yakeda yawancin hankuri da mutane a gari.
SHIBKAU: Namiji wanda aka haifa lokacinda ake shibka.
NOMAU: Namiji wanda aka haifa lokacinɗa ake noma.
SARKI: Ɗa mai sunan sarki. Namiji wanda ke da sunan sarki a masarauta.
Maifari ko Maihwari: Namiji wanda aka haifa lokacin fari.
Nagona, Nanoma: Namiji wanda aka haifa a gona.
HANA: Namiji wanda aka haifa a cikin gida lokacinda suke zaman makokin mutuwar dan gida ko yar gida.

TUNAU: Ana iya cewa “Tuni” ma’ana tunowa da haihuwa. Namiji wanda aka haifa bayan uwar shi ta ɗauki tsawon lokacin kafin ta sake ɗaukar ciki.
MAIKASUWA: Ɗan kasuwa ko mai kasuwa.
KASU, KASUWA: Ɗa namiji wanda aka haifa a kasuwa ko ranar kasuwa a gari.


KADAƊE: Ɗa namiji wanda aka haifa bayan uwaye shi sun daɗe basu taɓa haihuwa ba kafin daga bisani a haife shi.
TANKO: Ɗa namiji kanen mata a cikin ɗaki. 
JIKA: Jikan wani. Namiji wanda yakeda sunan jikan wani.
KANE: Karamin kanen wani. Namiji wanda yakeda sunan kanen wani.

MAIKUDI: Wanda yakeda kuɗi ko dukiya.
MADUGU: Ɗa namiji wanda aka haifa lokacin tafiya ko wanda aka haifa cikin yanayin tafiya.
KAKA: Mai sunan kakanni. Wanda yakeda sunan kakan wani.
TAGWAYE: Yayan da aka haifa su biyu kamar Hassan da Usaini.
GAMBO: Kanen yan tagwaye.
KOKARI: Mutum wanda yakeda yawancin kokari a gari.
FARI ko HWARI, JATAU: Namiji wanda yakeda fari kamarmadara.

NAHANTSI KO HANTSI: Namiji wanda aka haifa da hantsi.
KULAU: Namiji wanda aka fi so a ɗaki.
NAGOMA: Ɗa namiji wanda yake cikon na goma a ɗaki.
JIGO: SHUGABA. Ɗa namiji wanda aka haifa cikin magajinnai mata, kenan ya zamo shugabansu.
KARAMI: Mai karamin jiki ko karamin kanen wani.
GUNTAU: Guntun mutum.

JARIRI: Ɗa namiji wanda yakeda karamtar gaske lokacin haihuwa.
KORAU: Ɗa namiji wanda aka haifa lokacinda aka saki uwar shi.

SUNAYEN MATA NA GARGAJIYA:

ABARTA: Ɗiya macce wadda aka haifa bayan magajinnan ta duk sun rasu.

ARAGA: Ɗiya macce wadda ta rage a gida bayan yanuwanta na rasuwa.
BAKUWA: Ɗiya macce wadda aka haifa bayan an yi baki a cikin gida. Manufarsu shine tareda baƙin ta take.
DAƊE: Ɗiya macce wadda aka haifa bayan uwayenta sun yi shekaru da dama basu samu haihuwa ba.
DELU, DELA, KANDO: Ɗiya ta farko da aka haifa a ɗaki bayan magajinnan ta na ukku ko hudu duk maza ne. Kaunar maza ukku ko hudu a ɗaki.
KYAWO: Sunan da ake ba macce wadda takeda kyawon.
GASKE A GARI. Yarinya ko macce wadda ta razana hankalin maza lokacin tana budurwa.
MATA: Ɗiya macce wadda takeda sunan matar wani.

TANOMA: Macce wadda aka haifa lokacin noma.
UWANI: Mai sunan uwar wani. Ɗiya macce wadda takeda sunan uwar wani ko wata.
GIMBIYA: Mai sunan ɗiyar sarki. Ɗiya macce wadda takeda sunan ɗiyar sarki a masarauta.
KADADA: Ɗiya wadda uwarta da babanta dangin juna ne.
FARA KO HWARA: Macce wadda takeda haske kamar madara.
GWAMMA: Ɗiya macce wadda aka haifa bayan magajinnan ta na ɗaya da na biyu ko ukku duk matane a cikin ɗaki. Gwamma na nufin gwanda da aka haifeta da rashin ta.
HAKURI: Macce wadda takeda yawancin hankuri da mutane a gari.
KYAUTA: Kyauta daga Allah. Ɗiya ko ɗa tilo da ya rage bayan sauran na rasuwa.
RABO KO RABOCI: Rabo daga Allah, Ɗiya ko ɗa tilo da macce ta haifa a tsawon rayuwarta ta aure.
TSAKANI: Wadda ta zama ta tsakkiyat haihuwa a ɗaki.
YADA: Macce wadda aka haifa bayan yanuwanta na rasuwa amman ana wata al’ada dan ta tsaya.
TADAKA: Ɗiya macce wadda aka haifa lokacin da uwarta take daka.
TANOMA: Ɗiya macce wadda aka haifa lokacin ana noma.
YATSOHI: Ɗiya macce wadda uwayenta sun tsufa.

HANA: Ɗiya macce wadda aka haifa lokacinda yan gidansu ke zaman makokin mutuwar dan gida.
SAMU: Ɗiya macce wadda aka haifa bayan uwayenta sun ɗau lokaci mai tsawo kafin su samu haihuwa.
SHEKARA: Ɗiya macce wadda tayi shekara guda cikin cikin uwarta kafin a haife ta.
KULUWA: Ɗiya macce wadda aka fi kulawa da ita a gida da sauran wasu sunaye da dama.
KU SANI: Sauran gungun kabilun hausawa irinsu: Kanawa, Katsinawa, Zamfarawa, Hadejawa, Kabawa d.s.s mai yuwuwa nada nasu jerin sunayen na gargajiya ko masu ma’ana guda da waɗannan ko wanda suka sha bambam da waɗannan, dangane da yadda ake gayin su. Waɗannan sunayen an fi samunsu tsakankanin gobirawa, katsinawa, kabawa da zamfarawa.

IRE IREN WANDANNAN KUWA HAR YANXU MAGUZAWAN DA BASU KARBI ADDINI BA NA AMFANI DASU.

  • Jankare
  • Biju
  • Bodari
  • Ribau
  • Gubusani
  • Bauri
  • Gazawuri
  • Dangefe
  • Fasataro
  • Baƙin-bunu
  • Sammako
  • Ranau
  • Na Hantsi
  • Dare
  • Shuka
  • Nomau
  • Damina
  • Mairuwa
  • Anaruwa
  • Ci Gero
  • Ci Wake
  • Kosau

Tura Aiyukan Mu Zuwa daya daga cikin social media dake kasa Mungode

  1. Jalal says

    Tnk you

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »