TARIHIN JANAR MURTALA MUHAMMAD

1 1,266

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Ramat Muhammad

An haifi janar Murtala Muhammad aranar 8 gawatan Nuwamba a shekarar 1938 a cikin birnin kano,  yayi karatu a kwalejin barewa dake Zariya.

A shekarar 1959 ya shiga aikin soja, inda yayi karatu a makarantar Sojoji ta Royal Military Academic, ta standhursr, dake Burtaniya, Gabannin Dawowarsa Nigeriya a shekarar 1962, ya je rengadi a kasar Congo, a matsayin wani wakilin dakarun wanzar da xaman lafiya, Na majalisar dinkin Duniya.

A shekarar 1964 a ka bashi mukamin Manjo Na wucin Gadi, bayan da aka bashi ragamar kula da sashin sadarwa a hedikwatar rundunar sojoji ta Kaduna.


Janar murtala ya koma Lagos inda ya zauna tare da kawunsa, Alhaji Inuwa, Wanda a lokacin da aka bashi ministan Tsaro, kuma ya kasance a can har lokacin da akayi juyin mulki Na Farko, a shekarar 1966,
Shugaban kasa Manjo Janar Aguiyi Ironsi, ya karamasa girma I xuwa laftanal Kanal, koda yake shima Na wucin gadi ne, A watan Afrailu shekarar 1966, bayan juyin mulki Na farko, sau uku janar Murtala yake Neman hada kan Sojojin Arewa dake Lagos domin ayi juyin mulki Na biyu, sai dai wannan yunkuri bai yi nasaraba, bisa harbe wasu sojojin da akayi a Abekuta,

Janar Murtala Ramat Muhammad ya taka rewar gani a yakin basasar da akayi a shekarar 1967, lokacin da Laftanal kanal Ojukwu ke Neman balle yankin Biaffara saga Nigeriya,
A wannan lokacin janar Murtala ya jagoranci Sojojin da suka murkushe Sojojin Biaffara, tare da kawo karshen yakin basasar baki daya, Kamar yadda ya bayar da sanarwa a ranar 21 ga watan Satumba shekarar 1967. Yana matsayin birgediya ne na sojin da sukayi juyin mulki Na Uku A Nigeriya Suka Nada Murtala A matsayin Shugaban Kasa,.

Inda a watan Junairun shekarar 1976 aka karamasa matsayi zuwa Janar Mai Anini Hudu, wato kololuwa kenan. Har ila yau a wannan Lokaci Janar Murtala ya kirkiro da sabbin Jihohi, guda bakwai, yakuma bayyana bukatarsa Na mayarda babban Birnin Nigeriya zuwa Abuja, Da kuma alkawarin mika mulki ga fararen Hula a shekarar 1979


Tura Aiyukan Mu Zuwa daya daga cikin social media dake kasa

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

  1. usman says

    labarin yayi amma de…….

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »