TARIHIN MASARAUTAR ZAZZAU (ZARIA) KASHI NA BIYU

0 2,708

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

ACIGABA DA TARIHIN SARAUTAR ZAZZAU
A KASHI NA DAYA MUNTSAYA A

A kusa da Karni na 18th, Masarautar Zazzau ta rufe yanki waje 37,850 Sq MLs. Saboda haka, yana da muhimmanci mai karatu ya san cewa a ciki wannan lokaci, babban birnin mulkin ya canja daga Turunku zuwa Kufena (Dutsen kufta  za’a iya ganin sa daga gidan sarauta). 

ZAMU DORA

Saboda dogon zangon  Habe wanda suka zo a kusan karni na 19th saboda mamayar  Fulani tun a 1804. 

Biyo Bayan nasarar Malamin addinin Islama Wato Danfodio cikin 1804, wasu malaman Fulani masu daraja sun karbi tuta Wato alama (alamar iko ko izinin) don gudanar da mulki a wuraren da suke. 

Mallam Musa (Wanda ya kafa  daular Malawa a Zazzau) wanda ya zama mai  riqe da tuta a  Zaria, kuma ya kasance tare da Mallam Yamusa (wanda ya kafa daular  Bare-Bare a Zazzau) da Malam Abdukarimu (wanda ya kafa daular Katsinawa a Zazzau) a kan umarnin Danfodio. na zuwansa Zaria, wanda  wakilan sukayi ƙoƙarin shiga cikin birnin ta  Kofar Doka, lokacin da wannan ya zama mai wahala, sai suka hakura suka shiga ta Kofar Bai, wannan taron ya nuna alama mai tabatar da tarihin Zazzau. 

Zazzau wata matatara ce ta Tara bayi don turasu zuwa kasuwanni na arewacin Kano da Katsina, inda ake canza su bayin da gishiri tare da dibansu zuwa kasuwa ta arewacin Sahara. 

A cewar tarihi, a kwai addinin Islama a masarautar tun  kusan 1456, amma ya bayyana cewa sun yadu sannu a hankali, kuma al’amuran bautar gumaka sun ci gaba har lokacin da Fulani suka ci nasarar a 1808. A lokuta da dama a cikin tarihin, garin Zazzau ya zama kamar na makwabatan  jihohi  kamar su Songhai, Bornu da Kwararafa. 

Alhamdulillah

Karanta:

Tarihin Masarautar Zazzau Na 1

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »