TARIHIN KOFOFIN ZAZZAU (ZARIA) KASHI NA DAYA

3 6,174

Zazzau na da tarihi babba a cikin kasar hausa, kuma kowa yasancewa duk inda aka samu gari to dole a samu kofofin shiga wannan gari musanman ace garin yanada tarihi. Wannan dalili yasa muka leko garin zaria muka kuma dauki kofofinsa donyin bayani akansu

KOFAR BAI:
An ce ainihi, ana kiran tane da suna kofar Bayan gidan sarki. Daga baya aka yankewa ace mata kofar Bai. Kuma ta cikin tane mutanen yankin Bauchi ke shiga Zariya.

KOFAR DOKA:
Wasu sunce kofar ta samo asali ne daga bishiyar Doka dake wajajen kofar. Amma wasu sunce an saya mata wannan suna ne daga wani dogari mai tsaron ta mai suna Doka.

KOFAR GAYAN:
An ce an sanya mata suna ne daga tafkin Gayan wanda ke kudancin kofar saboda muhimmancin sa ga rayuwar mazauna birnin Zazzau.

KOFAR KUYAMBANA:
An ce zamanin Sarauniya Amina aka ɓude wannan kofa, lokacin da taje yaki garin kuyambana ta karɓe ikonsa, ta dora wani baranta ya zama hakimi a garin. Sai aka ɓuda kofar tayadda mutanen Zariya dana kuyambana zasu rinka saduwa da juna cikin sauki.

KOFAR TUKUR-TUKUR — ( KIBAU ) :
Da fari an sanyawa kofar suna ne daga dutsen Tukur-Tukur, kuma da haka aka santa tsawon lokaci.

Amma sai sunan kofar ya sauya zuwa Kofar Kibau/Kibo a zamanin da Sarkin Ningi Haruna ya kawo farmakin yaki Zariya lokacin mulkin sarkin Zariya Sambo. Zazzagawa suka shige cikin ganjwa tare da rufe kofa. Sadaukan Ningi kuwa sai sukayi ruwan kibiyoyiƴga birnin na Zariya.

Ta wannan kofa mutanen da suka ɓullo daga zamfara, kebbi, Yauri da Gobir suke shigowa Zariya. 

Mu kasance a kashi na biyu don karasa zayyano muku. 

Kuyi kokarin tura aiyukan mu zuwa social media 👍 dake kada

Kuna iya yin comment don tambaya

  1. ZAKARIYAU MUHAMMAD says

    MUN GODE

  2. abbasi says

    assalamu alaiku inamuku fatan alkairi

  3. Safiyya says

    Comment…muna godya matuka

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »