TARIHIN HARUNA UJI KASHI NA DAYA

0 4,129

TARIHIN HARUNA UJI KASHI NA DAYA

Alh. Haruna Uji Hadejia.
An haifi Alh. Haruna Uji a Unguwar Gandun sarki dake cikin garin Hadejia, a shekarar (1946). Sunan Mahaifinsa Mallam Ibrahim, Malami ne kuma shine Limamin Gandun sarki. Sunan Mahaifiyarsa Zainabu itama mutumiyar Unguwar ce. Anan ya tashi yayi wayo. Yana kimanin shekara shida mahaifinsa ya sakashi a makarantar Allo dake kofar gidansu, a gun wani Malami da ake kira Mallam Alhaji.
Haruna Uji ya shafe wajen shekaru uku yana wannan Makaranta a Gandun sarki, daga nan suka tashi da malaminsa zuwa garin Birniwa wanda take gabas da Hadejia, mai nisan kilo mita 45. Sun kwashe shekaru kamar biyu suna karatu da sauran Almajirai, anan Uji ya samu karatu mai dama.
Bayan nan suka bar Birniwa suka dawo Hadejia suka ci gaba da karatu a Gandun sarki. Wannan yasa ya samu karatu mai dama fiye da sauran yara musamman wadanda suka zauna a gida basu fita wani guri neman Ilmi ba. A wannan lokaci Mallam Alhaji yakan sa Uji ya kula da yara tare da koya musu karatu. Haruna Uji ya bar makarantar Allo yana dan shekara goma sha biyu, bayan ya samu karatu mai dama.
Hadejia A yau!
ASALIN INKIYAR HARUNA UJI..
Sunansa na yanka Haruna, yaci sunan wan Mahaifinsa, wato Mallam Haruna. Mallam Haruna mai sunan Uji yana da mata mai suna IYA KURA, Lokacin Uji yana karami matan kanin Babansa suna masa wasa suna ce masa Mijin Iya Kura, Mijin Iya Kura’ A wannan Lokacin yara kannensa basu da baki, sai suke ce masa, Ujin Iya Kura. Maimakon Mijin Iya Kura. Wannan shine Asalin inda Haruna Uji ya samo Inkiyar Uji. Tun ana danganta sunan da Iya Kura har aka daina ake cewa Uji.
SIFFAR HARUNA UJI.
Haruna Uji baki ne, mai matsakaicin tsawo, yana da jiki matsakaici, ga farin hakora da bakin gashi, yana yawan barin gashin baki, ga magana (Idanu) haka kuma, ma’abocin barin suma ne, yana da Murya mai zaki da kauri kadan, kuma Gwanin Ado ne, da manyan kaya na sarauta. Kuma yakan saka ‘yar shara, musamman lokacin zafi.
Alh. Haruna Uji mutum nd mai fara’a da kyauta, domin abin hannunsa bai rufe masa ido ba. Yana da raha sannan kuma bashi da wata nakasa a fili.
SANA’OIN HARUNA UJI..
FARAUTA DA NOMA.
Bayan Haruna Uji ya bar makarantar Allo, ya fara zuwa Daji da nufin farauta. Wadda itace sana’arsa ta farko, wanda ya fara, kuma ta sanyashi jarunta inda ya zama bashi da tsoro. Kuma a nan ne ya samu tambaya wato lakani na tsare kai.
Bayan farauta Haruna Uji Manomi ne, ya fara aikin gona ne da taya mahaifinsa, domin neman tabariki, wannan tasa yasan harkar noma wanda har yake noma gonar kansa.
SANA’AR SA
Alh. Haruna Uji yayi Sana’ar Tukin mota, wanda ya fara da Yaron mota a gun Mai gidansa wanda ake kira da suna Jibrin Dan Amingo. Jibrin Dan Amingo dan Asalin Danbatta ne ta Jihar Kano. Haruna Uji ya shafe shekaru da dama yana sana’ar yaron mota. Tukin mota ne sana’arsa ta farko da ta fara fitar dashi wani gari da nufin zama. Suna aiki ne tsakanin Kano da Hadejia.
Kuma a wannan lokacin suna zaune ne a garin kano a Tudun wada. Amma duk abinda ya taso a gida dashi akeyi, musamman aikin gona da bukukuwa da sauransu.
SANAAR WAKA
bai gaji waka ba, domin Mahaifinsa Malami ne, kuma ko a wakarsa ta Gurmi ba Haramun ba yana cewa:-
“Ni Haruna dan Mallam nake, Waka ta ba ta gado bace”
Saboda haka tun farko Haruna Uji ya riki waka ne a matsayin nishadi, domin ba wanda ya koya masa waka a matsayin Sana’a.
Haruna Uji ya fara ganin Gurmi ne a gun wani ma’aikacin titi wanda sukayi aiki a hanyar Mallam madori zuwa Gumel, wanda ake kira Dan-mato, a gun Dan-mato Uji ya fara ganin Gurmi da kidansa, shi Dan-mato yana kada Gurmi ne a yayinda suka samu hutun aiki. Yana kadawa yana waka, lokacin Uji yana Matashi, duk lokacinda sukaje kallon aiki sai su tsaya suna ganin kidan Gurmin Dan-mato, wannan tasa kidan Gurmi ya shiga ran Haruna Uji, idan ya dawo gida sai yakan nemi gwangwani da tsirkiya ya hada Gurmi yana kadawa. Har Dan-mato suka hada aikin hanya bai koyawa Uji Gurmi ba, sai dai Uji yana zuwa yana ganin yanda yake kadawa. Wannan tasa Uji ya dinga kwaikoyon Dan-mato tun bai iya ba har ya koya.
Wannan yasa idan yana gurmi yara sukan tsaya suna ji da kallonsa, Wannan shine Asalin koyon Gurmin Haruna Uji. Daga nan sai ya fara tunanin ya samu sanda, da lilo da butar Duma da fatar Damo da Zobe domin ya hada bubban Gurmi.
Farkon lokacinda ya fara Gurmi idan an bashi abu baya karba, don yanayi ne saboda Nishadi. Kuma sau da yawa idan ya fito hira ko ana wani biki na samari da ‘yan mata, yakan kada Gurminsa yana waka, samari da ‘yan mata suna kallo.
A wancan lokacin yana Gurmi yana aikin Mota, wannan yasa ya fara Gurmi a garuruwa daban daban na Arewacin Nigeria.
Daga nan Uji ya bar tukin mota ya koma kidan Gurmi Kuma ya nemi mataimaka don sunayi su biyu.
……. 
Littafin Muhd. Aji Hadejia
HADEJIA A YAU!
RUBUTAWA HADEJIAWA
Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »