ASSALIN WASAN BARKWANCI TSAKANIN KANAWA DA ZAZZAGAWA
Asalin abin akace watarana ne Sarkin Kano Bugayya ya fita yaki zuwa kasar Zazzau, ya tafi da jarumawan sa masu yawa ya doshi garin Turunku birnin Zazzagawa.
Tun kafin ya riski garin sai labari ya iske sarkin Zariya na lokacin Muhammdu Abu cewa ga kanawa nan suna zuwa Zazzau da yaki.
Wai dajin haka sai Sarkin Zazzau ya tara mayakansa suka dunguma zuwa wani wuri mai suna kufaina da shirin yaki, da zimmar su tari kanawa tun kafin su karaso Turunku. Da zuwa sai suka hau saman dutsen Kufaina suna jiran kanawa.
Lokacin da kanawa suka iso, tun daga nesa suka hango dakarun Zazzau a saman dutse, don haka kai tsaye sai suka tunkari gindin dutsen, sai jiyo mai shela akayi acikinsu yana shelanta cewa duk mutumin Kano ya nada gammo, zamu taru mu dauki dutsen kufaina tare da mutanen dake kansa mu tafi dasu Kano da sauri.
Daga nan sai kurum akaji kanawa sun dauki sowa suna fadin hobbasa! Hobbasa! Hobbasa! Akace dajin haka sai Sarkin Zazzau Muhammadu Abu yace ga mayakansa “Yaku Jaruman Zazzau, kada kowa ya motsa, wannan zambo ne na kanawa barayi mazambata. Ko aljanu basu iya daukan dutsen nan in ba mala’iku ba”.
Kunsan Zazzagawa (ga tsoro, kuma ba wayau), sai sukaki jin umarnin sarkin su. Suka rinka tsalle daga can kololuwar dutse suna tumowa kasan dutse, jikake tim. Wasu suka fado matattu, wasu kuma suka fado karyayyu,
wadansu kuma basu karye ba amma dai sun suma. Kanawa na ganin haka sai suka tattara sumammun da karyayyun sukayi awon gaba dasu izuwa Kano, akabar matattu yashe a gindin dutse, acan aka maishe su bayi bayan sun murmure.
Acan birnin Turunku kuwa, bayan kanawa sun janye jikinsu daga kasar Zazzau, sai Sarki Muhammadu Abu ya tarasu, yayi musu fada da gargadi akan kin bin umarninsa da sukayi. Yake cewa ku Zazzagawa kun bani kunya, me yasa kuka ki jin magana ta kukayi ta tsalle kuna fadowa gaban kanawa mazambata?
Anan ne sai wasu daga mayakan Zazzagawa suke cewa Ran sarki ya dade, yayin da mukaji kanawa na fadin hobbasa, sai mukaji tamkar sun daga dutsen, suna tafiya dashi izuwa kano. Mu kuma sai mukayi ta tsalle don bama so kanawa su tafi damu kano. Sai sarki yace wannan ai zambo ne irin na barayi.
Ance tun daga wancan lokaci aka samo wasan gargajiya wanda akeyi tsakanin Kanawa da zage-zage.
………..
Daga
LITTAFIN TASIRIN MAWAKAN BAKA WAJEN HABAKA AL-ADUN HAUSA
NA IBRAHIN MUHAMMAD