Tarihin Sana’ar Kira A Kasar Hausa Kashi Na Uku (3)

1 377

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

ABOKAN WASAN MAKERA

Bisa ga al’ada irin ta Bahaushe, akasarin sana’o’in Hausawa na gargajiya, suna da abokan wasa irin na barkwanci da ake gudanarwa tsakanin su a wannan sana’a da waccan. Kira ma tana da nata abokan wasan. Abokan wasan makera sun hadar da Buzaye da Wanzamai da Sharifai.

WASA TSAKANIN BUZAYE DA MAKERA

Wannan nau’i ne na wasan barkwanci da yake gudana tsakanin wadannan jama’a. Asalin wasan ya samu ne ta inda makera suke ikirari da cewa su ne iyayen dakin buzaye, domin sun ce, sune suke kafa gari. Bayan sun kafa sai Buzaye suzo su rabu da su domin samun abin masarufi. Haka kuma, Buzaye mutane ne masu ta’ammali da nau’o’in abubuwan da Makera sukesamarwa kamar takobi da azurfa da sauransu.

 Wannan shi ya haifar da wasan. Haka kuma, makera suna cewar su ne suke baiwa buzaye maganin wuta, wanda shi kuma Buzu yake cewar shi sharifi ne ya kuma rika wasa da wuta, ana bashi kudi. Daga bisani makera suke karya asirin maganin wutar da suke baiwa Buzaye. Saboda haka, idan Buzu ya je ya yi wasa da wuta sai yakone, sai yazo ya bawa Makeri hakuri da ‘yan kudi sannan kuma ya yarda cewar shi yaron ko bawan makeri ne, sannan Makerin zai sake bashi wani maganin. Wannan shi ne irin wasan da yake gudana a tsakanin Makera da Buzaye a Bahaushyar al’ada.

WASA TSAKANIN MAKERA DA WANZAMAI

Kasancewar sana’ar wanznuci sana’a ce da ta jibanci tuje gashi da cire shi da gyaran fuska da sauransu, wadannan ayyuka ba sa gudana sai da aska da ‘yar aska da koshiya matsagi da sauransu. Haka kuma Makera ne suke samar da ire-ire na barkwanci da kuma nuna tsatsuba tsakanin Makera da wanzamai. 

Makera kan ce “idan ba don su ba da wanzamai ba za su ci abinci ba”. Su kuma Wanzamai su ce ba haka zancen yake ba, nan da nan za a ga wanzami ya tugo zangarniyar dawa ko gero ko kuma ya balli reshen wata itaciya ya yi irin nasa tsatsibar ya kuma yi aski da shi.

Wannan shi ne irin wasan da yake wanzuwa tsakanin jinsin al’ummar guda biyu. Haka kuma abin yake wajen tallafa wa al’umma da magunguna irin na gargajiya. Wanzamai da makera kowa na alfahari da cewar ya san itatuwa daidai gwargwado.

WASA TSAKANIN MAKERA DA SHARIFAI.

Bahaushe ya yarda cewar duk mutumin da aka kira da suna Sharifi, to mutum ne babba mai daraja wanda kuma jika ne ga Annabi Muhammadu (S.A.W). Haka kuma Bahaushe ya hakikance cewa wuta ba ta cin sharifai domin tsatson da suka fito ya rabauta daga kunan wuta. 

Makera kuma mutane ne masu ta’ammali da karfe da kuma wuta. Ga su dai ba sharifai ba ne, amma kuma idan suna wasa da wuta kai ka ce sune sharifai, wannan shi ya haifar da wasa tsakanin Sharifai da Makera, tun da kowa yana tinkaho da wasa da wuta.

TASIRIN ZAMANI DA KIMIYYA AKAN SANA’AR KIRA

Kamar yadda bayani ya gabata cewa kira itace sana’a ta tsantsar hikima da fikira da basira da fasaha irin ta Bahaushe domin samar da duk nau’o’in abubuwan tallafawa rayuwa ta yau da kullum da ke tasarifi da karfe kimiyya da kerekere irin na zamani ya yi matukar tasiri mai amfani a kan wannan sana’a, domin kawo sauki wajen aiwatar da ita. Ire-iren tasirin da kimiyya da kerekeren zamani ke da shi kan sana’ar kira sun hadar da:

SAMAR DA GYARARREN KARFE

Bisa ga al’ada ta makera, sukan yi tafiya mai nisan gaske kafin su hako tamar da za su sarrafa, ta zama karfe domin gudanar da sana’arsu. Amma a yanzu, saboda kimiyya da kerekere irin na zamani, makera ba sai sun je garuruwa kamar Zazzau da Lokoja da Sakkwato da Ruruwai ba sannan su samo tama ko karfe ba, a yanzu zamani ya kawo karafa daban daban daga matattun motoci zuwa tsofaffin injinan mota cikin saukin kudi da kuma ba sai an sha wahalar hako tama ba.

Haka kuma, makera kan sha wahalar gaske wajn gutsuttsura karafa da daddatsa su, amma yanzu kimiyya irin ta zamani ta zo da wata irin na’ura mai fitar da iskar gas wai ita (carbide) da ake amfani da ita wajen daddatsa da kuma gutsuttura karfe cikin kankanin lokaci da kuma sauki. A nan kimiyya da kerekere irin na zamani yayi tasiri a kan sana’ar kira, domin akasarin makera a kasar Hausa sun koma amfani da irin wannan nau’ura domin saukaka wa kansu wajen gudanar da sana’ar kira.

Bugu da kari kuma, a da makera basa amfani da wani ajiyayyen ma’auni wajen auna tsawon ko fadin kayyayakin da suke samarwa. Amma yanzu kimiyya irin ta zamani ta zo da wasu abubuwa da ake amfani da su wajen auna tsawon abinda akeson a kera, misali (Ruler da tape measure) makera na amfani da su yanzu musamman wajen auna tsawo da fadi na kofa ko taga.

Haka kuma, sauran nau’o’in karafuna da a da, makeranmu basa amfani dasu. amma a yanzu, sakamakon kimiyya da kerekeren na zamani ya samar wa makeranmu irin wadannan karafa, misali (bronze da alminium), wato farin karfe da goron- ruwa duk yanzu makera na amfani da su wajen sarrafawa da samar da ingantattun abubawa domin tallafa wa rayuwar Bahaushe irin ta yau da kullum.

Haka kuma, a yanzu, makerarmu kan kwaikwayo wasu sassa na bangaren wasu na’urar casar gyada da makeranmu kanyi kwaikwayon irin wannan rariya ta na’urar casar gyada da sauran sassa na garmar shanu. Misali fikafikai da baki da kuma kundu na garmar shanun kanta. Haka kuma, a yanzu Makera na yin abubuwa daban – daban kamar irin su kwangirin zuba abincin dabbobi da tsuntsaye wadanda suka kwaikwaya daga Turawa.

Haka ma walda, hanya ce ta sarrafa karafa da zamani ya zo da shi, duk da cewa masu walda a kasar Hausa ba ainihin Makeran asali ba ne, itama walda tayi tasiri akan sana’ar kira a kasar Hausa.

Haka kuma tsirin zamani ya kara samarwa da masu sana’ar kira wasu hanyoyi don saukaka aiwatar da sana’ar su a cikin makera, 

Misali Zamu ga cewa samar da karfen kangarwa wadda ake wasu ‘yan dabaru ya rika bada iska ya rage masu wahala wajen amfani da zigazigi.

Haka kuma tasirin zamani ya samarwa da makera wani kalar gawayi wanda baya saurin mutuwa ko zama toka irin wannan gawayi ana kiransa da suna (magic coal). Sannan kuma a wasu wuraren suna amfani da batira su jona su da abin juyawa me dauke da ‘yar fanka (motor) domin ya bada iska cikin sauki.

KAMMALAWA

A takaice idan mukayi duba ga abubuwan da aka dudduba da kuma wadanda aka ambata a cikin wannan dan karamin bincike, zamu ga cewa anyi bayani a kan ra’aye-ra’ayen manazarta a kan ma’anar sana’a, sannan kuma anyi bayani a kan sana’ar kira tun da ga asalinta da kayayyakin da ake amfani dasu wajen yinta, da yadda ake yin ita kanta sana’ar, tare kuma da yin duba ga tasirin da aka samu na zamani, wanda ya hada da kimiyya a kan wannan sana’a ta kira.

DAGA:

Tsangayar Daukaka Harshen Hausa Da Al’adu Da Kuma Adabi, 

MANAZARTA

Musa H. Modibbo, (1979): “Ciniki da Sana’o’I a Kasar Hausa”. General Editor; Ibrahim Yaro Yahya. Thomas Nelson Publishers.

Muhammad Abdu Durumin-iya (2006) “Tasirin Kimiyya da Kare- karen Zamani A kan Sana’o’in Hausawa na Gargajiya”. Kabs Print Service (NIG).

Aminu M.S (1993) “Faduwar Sana’o’in Gargajiya a Zamanance”, Kundin Binciken na neman Digiri na farko.

Tattaunawa da Mallam Umaru Makeri da ke unguwar Yamadawa, ranar Talata 16th-09-2014, da misalign karfe 5:30

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

  1. […] TARIHIN SANA’AR KIRA A KASAR HAUSA NA 3 […]

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »