TARIHIN KASAR HAUSA

1 2,972

KASAR HAUSA

Kasar Hausa kamar yadda tarihinta ya zo a litattafai da dama,suna alakantata da mazaunin Hausawa na farko kafin su watsu zuwa sassa daban-daban na duniya.
 Mu’azu (1993:1) ya bayyana ainihin kasar Hausa ta asali da” tana Afirka ta yamma ne, a farfajiyar da ke tsakanin hamadar sahara da kuma dazuzzukan da suka doshi gawar tekun atlantika, watau daga kudu.Kuma ana kiran kasar da sunan  Sudan ta yamma,watau tafkin Chadi da kuma gwiwar kogin Kwara a  can yamma.”
A wani kaulin kuwa Dokaji (1978) ya bayyana kasar Hausa da  kasa ce da ta dade da wanzuwa a yammacin afirka wadda kuma ba a iya hakikance lokacin fara wanzuwarta.
 A cewar wasu masana, kasar  Hausa ita ce yankin nan na kasar Sudan wanda ke wajen tsakiya-tsakiya. 
Daga gabas da ita akwai kasar Borno, daga yamma kasar  Dahomey (wacce yanzu ake kira jamhuriyar Benin), daga arewa hamadar sahara, daga kudu kuma kasashen da ake kira “Middle  belt”
Alhasan (1982) Ya ce asalin kasar Hausa ya faro ne daga  kauyukan Lalle da Asodu da ke arewa maso gabas da Agadas can  cikin kasar Nijar.
 Daga can Gobirawa suka taso kadan kadan suka taru a muhallinsu na yanzu da ke cikin arewacin Nijeriya. 
DAGA LITTAFIN:- TASIRIN MAWAKAN BAKA WAJEN  HABAKA AL-ADUN HAUSA 
IBRAHIM MUHAMMAD (DAN MADAMIN BIRNIN – MAGAJI)
  1. Nazifi Ibrahim Shamakeri says

    Wannan tarihi ya fa’idantar sosai. Allah ya kara habaka Hausa, ya kuma kare Hausawa.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »