TARIHIN ALH. DR. DANMARAYA JOS NA 2

1 143

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

GOGAYYARSA DA GUDUNMAWARSA
Haƙiƙa, Ɗanmaraya mutum ne mai basira da kuma hazaƙa. Ya kuma samu gogewa sosai a harkar rayuwa. Mutumin da ya taso a gidan sarauta, daga baya kuma ya zama yaron makaɗa, a ƙarshe kuma ya vige da Karen mota, tofa ba makawa ya san maza kuma suma su san shi. Wannan kenan, bayan kuma zamowarsa Alhaji (Dr.) Adamu Ɗanmaraya Jos, ya ziyarci ƙasashen duniya manya da ƙanana. Daga cikin ƙasashen da ya ziyarta akwai: Barazil, Ingila, Amurka, Jammaika, Beniziwela, Bulgeriya, Bahamas, Kyuba, Baharain, Romaniya, Jamus, Babados, Holan (Holland), da sauransu (Habib, 2006; Malumfashi, 2015).
Mutum mai tarin gogayyar rayuwa irin wannan, ba zai rasa gudunmawar bayarwa. Tabbas, Alhaji (Dr.) Adamu Ɗanmaraya ya bada gagarumar gudunmawa wajen wayar da kan jama’a, ilimantarwa, kyautata tarbiya, nishaɗantarwa, da kuma yaɗa al’adu da havvaka yaren Hausa duka ta cikin waƙa. 
Kun ji abin da Umar (2015) ya ce: “… ya zamo wani ginshiƙi da makaɗan gargajiyar Hausa ke alfahari da shi, musamman idan aka yi la’akari da irin gudunmawar da ya bayar wajen yaɗuwa da ci gaban Harshen Hausa a nahiyar Afirka da manyan ƙasashen duniya”. 
Shi kuma Lalo (2015) cewa ya yi: “…Waƙoƙin Ɗanmaraya sun fi karkata ne wajen nuna matsalolin rayuwa, zamantakewa, shugabanci da yin nasiha musamman ga matasa da kuma zaman lafiya da wa’azi”. Ita kuwa jaridar Premium Times (2015), ta ruwaito wani makusanci mai suna Salihu yana cewa: “… ina alfahari da cewa ya yi rayuwa mai amfani, ya faɗakar da al’umma ta hanyar waƙa, kuma a fakaice ya cusa aƙidun Musulunci. Allah ya saka masa da Aljannar Firdausi”. Shi kuwa Alhaji Lawal Ishaƙ cewa ya yi: “…Waƙoƙin nasa, waɗanda suka fi mayar da hankali kan al’amarin jama’a, suna wa’azanarwa kan son juna da daidaito da kuma sauƙin hali”, Rev. Benjamin Kwashi ya ce: “…Waƙoƙinsa suna nishaɗantarwa tare kuma da ilimatarwa…”,
 Haka nan Alhaji Sani Mu’azu ya ce: “… Ba za a manta da Ɗanmaraya ba, saboda ya yi waƙoƙi masu tarin yawa wanɗanda ske karantar da dogaro da kai, juriya, gaskiya, kyakkyawar maƙwabtaka, haɗin kai da kuma jarumtaka”, (Yohaig, 2015). Allah ya yi masa sakayyar alheri.
WAƘOƘINSA
A tsawon rayuwarsa, Alhaji Ɗanmaraya Jos ya rera waƙoƙi masu tarin yawa. Waƙar da ya fara rerawa ita ce ta waƙar Karen mota, wacce ake yiwa laƙabi da waƙar “Malam na Baya” Duba varin dama na wannan shafi ka saurari wannan waƙar. Kaɗan daga jerin waƙoƙinsa akwai: 

1. Likita. 
2. Auren Dole. 
3. Gangar Ciki. 
4. Ɗan’adam. 
5. Talakawa. 
6. Mai Akwai da Babu. 
7. Waƙar Sana’a. 
8. Gangar Malamai. 
9. Siyasa. 
10. Haƙuri. 
11. Malalaci. 
12. Duniya. 
13. Ina Ruwan Wani. 
14. Ishara. 
15. Waƙar Aure. 
16. Bob Guy. 
17. Gulam Wuya. 
18. A Daina Shan Ƙwaya.
LAMBOBIN YABO
Bisa la’akari da irin wannan gudunmawa da ya bayar, Alhaji (Dr.) Adamu Ɗanmaraya ya samu lambobin girmamawa da suka haɗa da digirin digigir, da kuma lambar yabo ta zaman lafiya da Majalisar Ɗinkin Duniya ta bashi mai taken “United Nations Peace Medals” sannan kuma ya samu lambobin MON da OON daga Najeriya (Umar, 2015; Habib, 2006; Malumfashi, 2015).
RASUWARSA
Alhaji (Dr.) Adamu Ɗanmaraya ya rasu a ranar 20 ga watan Yuni na shkarar 2015 (20 June, 2015), bayan rashin lafiya da ya yi fama da ita. Allah ya jiƙansa da rahama. Amin. An bayyana rasuwarsa a matsayin babban rashi ga wannan duniyar bakin ɗayanta. Kakakin majalisar Dokokin Najeriya, honarabul Yakubu Dogara shi ya faɗawa ‘yan jarida haka (Umar, 2015; Ahovi da Abu, 2015).

DAGA SAHFIN: RumbunIlimi.Com.Ng

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

- Advertisement -

- Advertisement -

1 Comment
  1. Unknown says

    Ohh Duniya kenan
    Yau Kaine gobe ba kaiba
    Allah ya bamu ikon aikara Alkhairu

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »