TARIHIN ALH. DR. DANMARAYA JOS NA 1

0 147

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Ɗanmaraya, sunan da ya samo asali daga al’adar nan ta Hausa ta krain dukkan wanda mahaifansa biyu suka rasu yana ƙarami. Cikakken sunansa shi ne Adamu Muhammadu Wayya. Daga baya ya koma Alhaji (Dr.) Adamu Ɗanmaraya, aka kuma fi kiransa da Ɗanmaraya Jos.
Alhaji (Dr.) Adamu Ɗanmaraya mutumin kirki ne, fasihi kuma bajimin mawaƙin Hausa. Mutum ne mai kyauta, tausayi da kuma jarumtaka. Zuwan filin daga a lokacin yaƙin basasar Najeriya wanda aka yi a shekarar 1967 zuwa 1970, ya tabbatar da cewa shi jarumi ne. Alhaji Ɗanmaraya Jos ya je wannan filin daga da kuntuginsa yana yiwa sojoji waƙaoƙin ƙarfafa huiwa.
Mutum ne mai gogayya dangane da harkar rayuwa. Ya taso a gidan sarautar Bukuru ta Jos, ya kuma samu kansa a Karen mota. Allah kenan, me yadda ya so. Wato mutum ne da ya fara rayuwar jin daɗi, sai kuma ya girma a wani hali.
Ya rayu tsawon shekaru 69 a duniya. Har ya rasu, Allah bai hore masa ɗa ba. Amma duk da haka, ya riƙe marayun ‘ya’ya.
HAIHUWA
An haifi Ɗanmaraya Jos a garin Bukuru ta cikin Jahar Filato (Habi, 2006; Wikipedia, 2005; da kuma Lalo, 2005; Babayo, 2015). Amma Malumfashi (2015) ya musa hakan. Ya ce a Sakkwato aka haifi Ɗanmaraya. An haife shi a shekarar 1946.
Cikakken sunansa shi ne Adamu Muhammadu Wayya, daga baya ya koma Ɗanmaraya bayan rasuwar Mahaifansa biyu. Mahaifinsa, Muhammadu Wayya ya rasu lokacin Adamu yana jariri, haka nan kuma mahaifiyarsa mai suna Asta, ita ma ta rasu Adamu yana ƙarami. Bayan rasuwar waɗannan mahaifa nasa sai sunansa na Ɗanmaraya ya fara, sunan da dama al’ada ce a ƙasar Hausa ta kiran duk wanda ya rasa mahaifansa biyu yana ƙarami. Wannan suna, da shi ya shahara a duniya. Bayan girmansa kuma sai ya zama Alhaji (Dr.) Adamu Ɗanmaraya Jos, amma an fi kiransa da Ɗanmaraya Jos.
SALSALA
Alhaji Adamu Ɗanmaraya Jos, ɗa ne ga Muhammadu Wayya, wanda shi kuma asalin mutumin Sakkwato ne, kuma makaɗin sarakuna. Sana’arsa ta kiɗan kotso ta kais hi fadar sarkin Bukuru Alhaji Muhammadu ya yi kiɗa, bayan ya yi kiɗa sais hi sarkin Bukuru ya buƙace shi da ya ƙaura ya koma can da zama ya zama makaɗinsa (Malumfashi, 2015; Habib, 2006).  
TASOWARSA
Alhaji Adamu Ɗanmaraya ya taso a gidan sarautar Bukuru, ƙarƙashin kulawar sarkin Bukuru Alhaji Muhammadu. Sarkin Bukuru ya saka shi a makarantar koyon karatun Alƙur’ani tun yana ƙarami. Haka nan da ya isa munzali an saka shi a makarantar elemantare (elementary), makarantar da bai samu nasarar kammala ta ba. Habib (2006) ya ruwaito cewa Alhaji Adamu Ɗanmaraya a ɗaya daga cikin irin hirarrakin da ake yi da shi ya bayyana cewa sarkin na Bukuru ya riƙe kamar ɗan cikinsa.
Lokacin da Ɗanmaraya ya kai shekara shida a duniya, sai sarkin Bukuru ya ɗauko masa ganganunan da mahaifinsa ya rasu ya bari, ya bashi, ya kuma yi masa bayani cewa ga asalin mahaifinsa kuma sana’arsa ita ce waƙa. Wannan abu shi ya dasawa Ɗanmaraya sha’awa da kuma son waƙa da kuma burin ganin ya gaji mahaifin nasa.
Bayana rasuwar sarkin Bukuru, sai Ɗanmaraya ya shiga halin rashin mai kulawa. Yana nan cikin wannan hali, sai wata mawaƙiya mai suna Zabiya Mamu ta je garin Bukuru tare da wasu yara guda biyu waɗanda suke jikoki ne a wajenta. Su waɗannan yara suma ‘ya’yan wani mai kiɗan kotso ne ya mutu ya bar su. Shike nan, sai Ɗanmaraya ya samu abokan yawo. Ya riƙa binsu suna tafiya su je su yi kiɗa da waƙa a basu ɗan abun hasafi, idan aka basu sais u kaiwa wannan mata wacce ke riƙe da su.
Wata ranan ana cikin wannan hali, sai wannan mata ta yi nufin tafiya Makka dan sauke farali. Da ta tashi tafiya sai ta tafi da waɗannan yara guda uku; wato har da Ɗanmaraya kenan (Habib, 2006). Da suka tashi tafiya sai suka biya ta garin Bauci, inda suka tsaya suka yada zango na wasu kwanaki. Daga nan sai suka ɗau hanyar su ta zuwa Maiduguri, inda  a nan Ɗanmaraya ya fara ganin mai kuntugi (Habib, 2006; Malumfashi 2015). Daga nan kuma kiɗan kuntugi ya fara shiga ransa.
Da suka isa Maiduguri sun zauna kusan tsawon shekaru uku. A cikin wannan zama ne ya samu ya fara koyon kiɗan kuntungin, shigarsa wannan fannin kiɗa na kuntugi, sai kuma savani ya fara shiga tsakaninsu da Zabiya Mamu da yaranta, saboda haka sai ya rabu da su ya dawo gida.
Da Ɗanmaraya ya dawo gida sai kuma ya kama sana’ar karen mota, sannan kuma a lokaci guda yana tare da kuntuiginsa. Duk gunda mota ta tsaya, sai ya fito da wannan kuntugi nasa yana waƙa, jama’a kuma suna sauraro suna kuma bashi ɗan abinda ya samu. Da haka, da haka, sai Gudunmawarsa. 

DAGA SAHFIN: RumbunIlimi.Com.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

- Advertisement -

- Advertisement -

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »